Mutane 36,000 sun ƙi amsar rigakafin Korona a Birnin Kudu

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse

Lissafi ya nuna kimanin mutane  36,000 ne suka ƙi amsar allurar rigakafin cutar Korona a yankin Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ke jihar Jigawa. 

Jawabin hakan ya biyo bayan wata ziyara da kwamatin kiwon lafiya mai karfin gaske ya kai ziyara ƙaramar hukumar domin ganin an yi gangami wajen nuna wa jama’a muhimmancin rigakafin Korona.

Kwamitin a ƙarƙashin jagorancin babban Sakataren Hukumar Lafiya kuma muƙaddashin kwamashinan lafiya na Jihar Jigawa Dr Sambo Ibrahim tare da manyan muƙarrabansa a hukumar lafiya matakin farko sun je ƙaramar hukumar ta Birnin Kudu domin gano kura-kuran dake ƙaramar hukumar akan yadda jama’a suka ƙi amsar allurar rigakafin a yankin.         
          
Kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na ƙaramar Hukumar Birnin Kudu, Malam Nasiru Yusuf Birnin Kudu ya ce sun gano kimanin mutane 36,000 ne suka ƙi amincewa a yi masu allurar rigakafin cutar ta Korona a yankin ƙaramar hukumar.

Saboda haka ne ma Babban Sakataren Hukumar Lafiya Dr. sambo Ibrahim ya buƙaci ƙaramar Hukumar Birnin Kudu da ta basu haɗin kai don ganin sun kai ga samun biyan buƙatar da suka sa a gaba na aiwatar da rigakafin ga ɗaukacin al’ummar yankin.

Sambo ya kuma yaba wa ƙaramar hukumar akan yadda ta taimaka wajen ganin sun yi nasara akan allurar foliyo a yankin.         
         
Shi ma da yake mayar da martani, Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu Alhaji Magaji Yusuf Gigo ya ce ƙaramar hukumarsa ta bada gudunmawar kuɗi sama da Naira dubu ɗari biyar a matsayin gudunmawar ta don ganin shirin allurar rigakafin Korona ya yi nasara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *