Mutane biyar sun mutu sanadiyyar ruftawar ƙasa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Aƙalla mutane biyar ne su ka mutu a yayin da ƙasa ta rufta musu lokacin da su ke haƙar ta don yin gini.

Mutane biyar ɗin mazauna ƙauyen Ƴanlami a ƙaramar hukumar Bichi sun gamu da ajalinsu a a ranar Asabar da ta gabata.

Mutanen da su ka mutu sun haɗa da Muhammad Sulaiman mai shekaru 35, da Jibril Musa mai shekaru 30, sai Masa’udu Nasiru mai shekaru 25 sannan Jafaru Abdulwahab mai shekaru 30 sai kuma Alasan Abdulhamid mai shekaru 22 a duniya.

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano SFS Saminu Yusif Abdullahi ya rabawa manema labarai, ya ce matasan sun tafi haƙar ƙasar ne domin gina wa abokinsu gida wanda ya ke gab da angwancewa.

Ya ce jami’an su sun isa wurin bayan karɓar kiran waya daga wani Malam Sanusi da ke Badume,

Tuni dai hukumar ta miƙa gawarwakin mutanen ga dagacin Ƴanlami a ƙaramar hukumar Bichi domin yin jana’izarsu kamar yadda addini musulunci ya tanada.