Mutane da dama sun rasu bayan tirela ta ƙwace a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Mutane da dama sun rasa rayukansu a yayin da wata tirela ta ƙwace a gadar Muhammadu Buhari dake Jihar Kano.

Haka kuma wasu sun samu raunuka a yayin da iftila’in ya auku da motar, wadda ta nufi Kudancin Nijeriya a yau Juma’a.

Kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Yahaya Abubakar Sadiq ya wallafa, ya ce lamarin ya faru ne daga Mariri a Hotoro zuwa Unguwa Uku inda tirelar ta kife ɗauke da mutane sama da 20 da wasu kayayyaki.

Wani shaida mai suna Shu’aibu Hamisu ya ce motar ta ƙwace ne daga hanyar Maiduguri a lokacin da direban ya yi ƙoƙarin sauya hannun zuwa titin Zaria.

A lokacin da aka yi ƙoƙarin ji ta bakin kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce suna aikin tattara bayanai game da al’amarin wanda nan ba da jimawa ba za a fitar da su.