Mutane uku sun mutu bayan da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita gidaje 495 a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano, SEMA, ta ce ambaliyar ruwa ta kashe mutane uku tare da raba iyalai 495 da muhallansu a Ƙaramar Hukumar Ajingi da ke jihar.

Babban Sakataren hukumar, Dr. Saleh Jili ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ajingi, yayin da yake raba kayan agaji ga waɗanda abin ya shafa, ciki har da iyalan mutum uku da suka rasu.

Jili ya lissafa yankunan da lamarin ya shafa da su ka haɗa da Toranke, Kara Malama, Chuna da Balare.

Ya ce lamarin da ya faru bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ranakun 3 da 4 ga watan Agusta, ya shafi mutane 495 da lamarin ya rutsa da su, ya kuma kashe uku da jikkata mutum ɗaya.

“A madadin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, mun zo nan ne domin jajentawa waɗanda abin ya shafa tare da raba musu wasu kayayyaki.

“Muna fatan wannan karamcin zai kawo musu ɗauki tare da rage musu raɗaɗi,” inji shi.

Kayayyakin da aka raba sun haɗar da shinkafa, masara, siminti, kwanon rufi, ƙusoshi, man girki, matashin kai, wake da katifu da dai sauransu.

Jili ya shawarci mazauna yankin da su riƙa gyara magudanun ruwa a kodayaushe, inda ya kuma yi kira ga waɗanda ke kusa da koguna da tafkunan jihar da su bar yankin.