Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Lawal Daura, ya ce wasu daga cikin mutanen da suka kewaye marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne suka ci amanarsa, lamarin da ya taimaka wajen jefa gwamnatinsa cikin matsaloli.
Daura ya ce abubuwan da suka faru a lokacin gwamnatin Buhari sun nuna haɗarin bai wa alaƙar mutum da amana fifiko wajen naɗa mutane mukaman gwamnati, ba tare da la’akari da ƙwarewa da cancantarsu ba.
Tsohon shugaban DSS ɗin ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Politics Today na Channels Television, wadda aka watsa ranar Litinin.
A cewarsa, Buhari ya kewaye kansa da mutanen da yake amincewa da su, amma daga baya wasu daga cikinsu suka kasa riƙe amanar da ya ba su.
Daura ya bayyana cewa kusancinsa da Buhari ya samo asali ne daga nauyin da ke kansa a matsayinsa na shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa, ba wai saboda kasancewarsa cikin wani rukuni na masu iko a gwamnatin ba.
Ya kuma kare tsohon shugaban ƙasar daga masu bayyana gwamnatin Buhari a matsayin mafi muni a tarihin siyasar Nijeriya, inda ya buƙaci masu sukar gwamnatin da su duba tarihin ƙasar daga shekarar 1995 zuwa lokacin da Buhari ya bar mulki a 2023, domin tantance waɗanne shekaru ne suka fi fuskantar matsaloli.
Daura ya shawarci gwamnatocin da za su zo nan gaba da su raba aminci da alaƙar mutum da kuma ƙwarewa da cancantar da ake buƙata wajen naɗa mutum a wani muƙamin gwamnati.
