Mutum 10 sun mutu a haɗarin jiragen sama masu saukar ungulu a Malaysia

Mutane 10 ne suka mutu a lokacin da wasu jirage masu saukar ungulu na sojojin Malaysia biyu sun yi karo da juna, yayin wani atisaye da suke yi.

Babban jami’in gudanarwa na hukumar kwana-kwana da aikin ceto ta ƙasar, Suhaimy Mohamad Suhail ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Firaministan ƙasar Anwar Ibhrahim ya miƙa saƙon ta’aziyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a haɗarin da ya bayyana a matsayin mai tada hankali, inda ya ce za a gudanar da bincike don gano musabbabin faruwansa.

An gayamin cewar ma’aikatar kula da harkokin tsaro za ta gudanar da bincike, musammanma rundunar sojojin ruwa ta ƙasa TLDM, don gano musabbabin farun haɗarin.

Ba kasafai aka cika samun aukuwar haɗarin jiagen sama masu saukar ungulu a ƙasasshen da ke shiyar Kudu maso Gabashin nahiyar Asiya ba.

Amma a watan da ya gabata, wani jirgin sama mai saukar ungulu na jami’an da ke tsaron gabar ruwan Malaysia ya yi haɗari a mashigar Malacca, duk da dai ba a samu asarar rai ba.

Haka nan a shekarar 2016, akwai mataimakin ministan ƙasar da ya rasa ransa a wani haɗarin jirgin sama mai saukar ungulu a Jihar Sarawak da ke ƙasar.