Mutum 16 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas a Afirka ta Kudu

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga ƙasar Afirka ta Kudu sun ce, wasu mutum 16 sun mutu sakamakon shaƙar iskar gas.

An danganta lamarin wanda ya auku a ranar Laraba a Boksburg da ke gabashin Johannesburg, da yoyon tukunyar gas a yankin.

Bayanai sun nuna an samu yoyon tukunyar gas ɗin ne sakamako haramtattun ayyukan masu haƙar zinari a yankin.

Jami’an yankin sun ce waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da mata da ƙananan yara.

Kazalika, sun ce samfurin gas ɗin da ya yi wannan ta’asar, wato ‘Nitrate oxide gas’, galibi da shi masu haƙar ma’adinai ta haramtacciyar hanya ke amfani wajen gudanar da ayyukansu.

Sun ƙara da cewa, an tsinci ɗaya daga cikin tukwanen gas ɗin da masu aikin haƙar madinai a yankin suke amfani da su tana yoyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *