Mutum 3 sun mutu a harin da aka kai ofishin NNPP a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano

Rundunar ‘Yan Sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutum biyu yayin da ake tsaka da tattara sakamakon zaɓe a ƙaramar hukumar Tudun Wada dake jihar kano.

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, CP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar a ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Sanarwar ta ce an sami bayanai cewa ana cikin tattara sakamakon zaɓen a Tudun Wada ne cikin ofishin hukumar zaɓe na ƙaramar hukumar wasu gungun ‘yan dabar siyasa suka kai hari a ofishin kamfen na ɗan takarar majalisar tarayya tare da cinna masa wuta.

Sanarwar ta ƙara da cewa nan take mutum biyu da ba a iya tantance su da motoci a cikin gurin suka kone ƙurmus sakamakon wutar da aka banka wa ofishin.

Kazalika, ‘yan dabar sun kuma tare hanyar zuwa ofishin hukumar zaɓe dake ƙaramar hukumar ta Tudun Wada.

Amma cikin nasara jami’an tsaro sun tarwatsa su, tare da jikkata ɗaya daga cikin maharan, wanda bayan an ɗauke shi zuwa asibiti don yi masa magani rai ya yi halinsa.

Haka nan, ‘yan sanda sun kama wasuutum huɗu da ale zargi da hannunsu a ta’asar.

A hannu ɗaya, rundunar ‘yan sandan Kano ta ƙara nasarar da cafke mutum huɗu da ake zargin hannunsu wajen kai farmaki da yunƙurin cinna wuta a ofishin hukumar zaɓe dake ƙaramar hukumar Takai.

Rundunar ta ce jami’an tsaro sun ƙoƙarta wajen daƙile kai harin, kana sun damƙe wasu da ake zargi da yunƙurin kai harin.

A ƙarshe sanarwar ta tabbatar da samun damar cigaba da tattara sakamakon zaɓe tare da kammalawa cikin kwanciyar hankali.