Mutum biyu sun mutu a faɗan manoma da makiyaya a Jigawa

‘Ƴan sandan Jihar Jigawa sun tabbatar da faruwar wani rikici tsakanin manoma da makiyaya. Abun ya faru ne a ƙaramar hukumar Birnin Kudu, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu da ƙona gidaje uku.

Shaidun gani da ido sun shaida cewa, wasu makiyaya sun gayyato makiyaya daga Jihar Katsina, wanda hakan yayi sanadiyar dabbobin su ke shiga gonaki suna yin ɓarna. Wannan ne yasa manoman su kayi ganganmi domin kare gonakin su.

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya bayyana cewa, yanzu haka yan sanda, da bigilanti, da sibil defens sun yi kokarin kawo lumana wajen. Yace sunyi nasarar watsa mutanen, da kamo shanu guda 15.

Yace rikicin yayi sanadiyar mutuwar mutum 2, wanda a yanzu haka sun cafke mutum biyar waɗanda ake tunanin suna da hannu a tashin rikicin.