Mutum da gaɓɓansa (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

‘Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin  ɗan-Adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda ƙirar jikinku ta ke da kuma yadda take aiki. 

Mu je kogon ƙugu:
Akwai abubuwa masu matuƙar muhimmanci a ciki irinsu mahaifa, bututun wucewar maniyyi, hanyoyin jini, da sauransu. Idan muka ɗauki mahaifa misali, za mu shafe tsawon lokaci muna bayani akanta. Abubuwan da suka shafi mahaifa sun haɗa da yadda take ɗaukar ciki, yadda take samar da jinin haila da na biqi, da yadda take sifarta ke sauyawa a tsawon rayuwar mace; wato yadda take a lokacin mace tana ƙarama, da adda take lokacin da mace take budurwa, da kuma yadda take lokacin da mace ta tsufa. Sauran abubuwa da zamu sani game da mahaifa su ne: girmanta, nauyinta, tsawonta, faɗinta, bigirenta, maƙwabtanta, kamanninta, yanayin zamanta, da kuma matsalolin da ke tasiri akanta. Wannan wani babban fage ne kuma zai ci shafukan rubutu masu yawa. 

Ƙafafu:
Kasangallen qafa ya rabu gida 4: ɗuwainiya, cinya, ƙauri, da kuma ƙafa. Ɗuwainiya cike take da tsokar nama wadda ke taimakawa ɗan adam wajen yin tafiya da kuma yayin zama. Akwai wata jijiyar laaka da tabi ta ɗuwainiya wadda idan aka samu ma’aikacin lafiya wanda bai san yadda jikin mutum yake ba, yayi allura akanta, to ƙafa za ta iya shanyewa. Cinya ita ma tana da tsokar nama mai yawa, kuma ta rufe ƙashin cinya a tsakiya. Shi yasa karaya a cinya take da wahalar sha’ani saboda naman da ke wajen yana da yawa.

Tsakanin cinya da ɗuwainiya, akwai mahaɗar ƙashin ƙugu; haka kuma tsakanin ƙashin cinya da na ƙafa, akwai mahaɗar ƙashi da ake kira gwiwa. mahaɗar gwiwa na daya daga cikin manyan mahaɗar ƙashi masu muhimmanci a jikin ɗan adam. Kuma wannan waje shi ne ke ɗauke da nauyin jikin mutum, musamman lokacin da yake a tsaye. Wannan mahaɗar ƙashi ta gwiwa, kamar alharga take, wato za a iya buɗe ta, kuma kuma a rufe ta, amma ta fuska ɗaya. Misali, Idan aka ce za a buɗe alharga ta ɓangaren ta yake a kafe (ɓangaren da baya motsi, inda aka kafe alhargar), to sai dai in karya alhargar za a yi. Haka ma mahaɗar gwiwar mutum. Lokacin da mtum a ke a tsaye kyam, gwiwarsa/ta a kulle ta ke.

Ga yadda abin yake: ƙoƙon gwiwa zai muskuta gefen waje, shi kuma ƙashin ƙauri wanda yake naniƙe da ƙoƙon gwiwa zai muskuta ciki, ta haka, sai gwiwar mutum ta kulle domin ya samu damar tsayawa kyam. Amma yayin da yake tafiya, ana buɗe gwiwar qafar da ta rabu da ƙasa (a ɗan tanƙwasa ta), sannan a kulle gwiwar da ke kan ƙasa domin ta ɗauki nauyin jiki. Za ku iya gwada tafiya tare da lura da abin da na faɗa anan. Za ku ga hakane. Ta haka ne ɗan adam yake samun yin tafiya ba tare da ya buƙaci wani gwaggwavan taimako daga tsoka ba. Amma fa duk da haka, yayin da ɗan adam ya yi taku ɗaya, an ƙiyasta cewa tsokar nama sama da guda 80 sun motsa. Wani aikin sai Rabbani!

A ƙafa da akwai tafin ƙafa, da kuma bayan ƙafa. Yanayin siffar hannu da ƙafa suna kama da juna, sai dai sun saɓa wa juna yayin da suke juyawa tun a lokacin da mutum da yake cikin uwa. Shi hannu ya juya ‘waje’ ne, shi yasa babban yatsa yayi nisa daga tsakiyar jiki. Ita kuwa ƙafa ta juya ‘ciki’ ne, shi yasa babban yatsa yafi kusa da tsakiyar jiki.

Na zubo bayani tun daga kai har zuwa ƙafa game da waɗansu manyan abubuwa da na sani. Amma na manta ba ɗanyi bayanin yadda jikin mutum yake a dunƙule ba. Tsawon ɗan adam, da nauyinsa, da muhallin da yake raye na da matuƙar tasiri wajen lafiyarsa. Haka kuma cimarsa, muhallinsa, da ƙwayoyin halittar da ya gada daga kakanninsa na da alaƙa da lafiyarsa, kaifin tunaninsa, muradansa, da kuma hazaƙarsa.

Ɗan adam kan yi wata tara a cikin uwa, kafin a haife shi. A wannan wata tara, akwai matakai na halitta iri iri da suke faruwa waɗanda wajibi ne saninsu a wajen ma’aikata lafiya, musmman likitoci da malaman jinya.  Tun daga ranar farko da maniyyi ya haɗu da ƙwan mace a cikin mahaifa, ma’ana shigar ciki, zuwa samuwar gaɓɓai, zuwa samuwar mabiyyiya, da girman ɗan tayin har zuwa haihuwarsa abubuwa ne masu matuƙar ban ta’ajibi. Muna fatan kawo waɗannan bayanai ɗaya bayan ɗaya.

Lokacin da ɗan adam yake a cikin uwa, daga ranar farko zuwa cikarsa wata biyu a ciki, an wassafa wannan lokaci da cewa shi ne mafi haɗari a rayuwar ɗan tayin mutum; saboda a lokacin ne ake samar da duk wata gaɓa kamar ƙasusuwa, zuciya, ƙwaƙwalwa, ƙoda, tsoka, da dai sauran gaɓɓai. Daga wata na biyu zuwa sama, gaɓɓan sukan ƙara girma da keɓance kansu da ayyukan da suka shafe su. 
Idan mace mai juna biyu tana shan giya ko taba sigari, hakan kan iya cutar da ɗan cikin, musamman idan bai fi wata biyu da samuwa ba!

Jikin ɗan adam yana da tsari sosai. Tsarin yadda jikin mutum yake rubutu ne mai zaman kansa shima. Shi yasa Allah bai yi nonon mace kusa da dubura ba, kamar yadda Ya yi wa akuya, tinkiya, da danginsu. Kuma shi yasa bai maka ido a goshi ba, ko kuma ƙofar hanci guda ɗaya ba. Amma da akwai wasu abubuwa da ke sa a haifi yaro da ido ɗaya, ko da ƙofar hanci ɗaya, ko kuma ma fuskar sulungudun ba tare da ido, hanci, ko baki ba. Haka na faruwa ne yayin da wani abu mai cutarwa a riski ɗan tayin a lokacin da yake ƙasa da wata biyu a cikin. Mu bar nan haka.

Yanzu bari mu kalli yadda mu’amala ke kasancewa tsakanin jikin ɗan adam da muhallinsa. Kamar adda na faɗa: jikin ɗan adam ba ya son baƙi; to amma a kewaye yake da su.


Yadda za ku yarda cewa jikin ɗan adam bayan son baƙi : ka bari ƙwaro ko kura ta shiga idonka ka gani me zai faru? A cikin ‘yan daƙiƙa idon zai yi ja! Haka kuma idan qura ta shiga bututun iska da maƙogwaro, za ku ji mutum yana ta tari, wani lokacin ma hadda khaki a ƙoƙarin fitar da abinda aka shaƙa.

Ka taɓa tsintar kanka a waje mai sanyi sosai? Ya kayi? Ina tunanin kin yi a ƙoƙarin rufe jikinka domin ki samu ɗumi ko? To, ƙudirin shi ne a taskance ɗumin jiki domin kada hada-hadar ayyukan jiki ta tsaya, a hanyar rawar ɗari. Ƙwarai kuwa! rawar ɗari ma da ranarta: tana taimakawa wajen samar da ɗumi ga jikin ɗan adam ya yi da ake tsananin sanyi.

Ka taɓa tsintar kanka a wajen mai zafi sosai? Ya kaji? Kuma a kayi? Ƙila ka fara zuffa sosai, wanda hakan ke taimakawa wajen saisaita zafin jiki. 
Jin tsoro, da ƙarfin hali, da jin dadi (na saduwa) duk abubuwa ne daga waje da suke kawo sauye-sauye a cikin duniyar jikin ɗan adam.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *