Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Daƙile Yaduwar Cutar Kanjamau ta ƙasa NACA ta bayyana cewa tana hasashen cewa mutum miliyan biyu ne ke ɗauke da cutar ƙanjamau a Nijeriya inda mutum miliyan 1.6 daga cikin su ke karɓar maganin cutar a ƙasar nan.
Shugaban hukumar Temitope Ilori ta sanar da haka a zaman da ta yi da masu ruwa da tsaki kan shirin ranar cutar ta shekarar 2024 da aka yi a Abuja.
Ilori ta ce daga cikin mutum miliyan biyu ɗin da hukumar ke hasashe sun kamu da cutar hukumar na da tabbacin mutum miliyan 1.4 masu shekaru 15 zuwa 64 dake ɗauke da cutar.
Ta ce sakamakon binciken UNIAIDS na shekarar 2023 ya nuna cewa aƙalla yara 160,000 masu shekara 0 zuwa 14 sun kamu da cutar a Nijeriya.
“Binciken ya kuma nuna cewa mutum 22,000 sun kamu da cutar sannan cutar na ajalin mutum 15,000 duk shekara.
“Duk da ci gaban da aka samu a yaki da cutar hukumar ta samu nasarar kare yara ƙasa da kashi 33 daga kamuwa da cutar sannan burin da hukumar ke neman samu shine kashi 95 nan da shekarar 2030.
Daga nan shugaban hukumar ta ce bana NACA za ta bada ƙarfin ta wajen kare yara kanana daga kamuwa da cutar.
“Hukumar za ta bada karfinta wajen wayar da kan mutane musamman mata tare da inganta matakan dakile yaɗuwar cutar domin tabbatar da cewa wadanda suka kamu da cutar na samun wurin karban maganin cutar.
Kodinatan UNIAIDS Leo Zekeng ya yi kira ga gwamnati da ta ware isassun kudade domin yakan cutar a kasar nan musamman ta fannin samar wa yara kananan kariya daga kamuwa da cutar.
Kodintantan PEPFAR ta Kasa Fumi Adesanya ta yi kira ga gwamnatin kasar nan, kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen kasarnan, fannin dake zaman kansu, kungiyoyin Kare Rajin Dan Adam da su hada hannu gaba daya domin yakan cutar daga kasar nan.
Ranar daya ga watan Disamba na kowace shekara ne aka kebe domin ranar tunawa da cutar ƙanjamau ta duniya.
An keɓe ranar domin wayar da kan mutane game da cutar domin hakan zai taimaka wajen daƙile yaduwar cutar.
Taken taron bana shine ‘ɗaukan matakin da ya kamata, haƙƙina na ne na inganta lafiyata”.
Bana Nijeriya ta yi wa taron taken “ɗaukan matakan da suka dace domin daƙile yaɗuwar cutar a tsakanin yara ƙanana daga nan zuwa 2030.