Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani rahoton na Cadre Harmonise game da mummunan matsalar abinci a Nijeriya ya yi hasashen cewa, mutane miliyan 30.6 a faɗin Jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya za su kasance cikin wani yanayi na ƙarancin abinci tsakanin watan Yuni da Agusta.
Rahoton wanda gwamnatin tarayya da gwamnatocin Jihohi tare da tallafin Hukumar Abinci da Aikin Noma ta FAO da sauran ƙungiyoyin raya ƙasa suka gudanar, ya nuna cewa adadin ya haɗa da ‘yan gudun hijira 150,978.
Ta bayyana cewa, duk da raguwar farashin abinci da kayayyakin masarufi a faɗin ƙasar, kimanin mutane miliyan 24.9, da suka haɗa da ‘yan gudun hijira 116,765 a jihohi 26 da Abuja, a halin yanzu suna cikin halin ƙarancin abinci, wanda ka iya taɓarɓare a watan Mayun 2025.
Binciken na CH ya yi hasashen cewa a lokacin bazara daga watan Yuni zuwa Agusta, iyalai za su fuskanci ƙarancin abinci, yana mai ƙarawa da cewa ƙalubalen yanayi na iya tura aarin yawan al’umma a yankunan da ke cikin haɗari zuwa cikin mawuyacin hali na matsalar abinci.
Rahoton ya danganta lamarin da tashe-tashen hankula da rikice-rikicen, gami da sake fasalin tattalin arziki, ya ƙara da cewa gidaje na iya fuskantar ƙarancin ƙarfin saye da kuma ƙarfin iya samun isasshen abinci.
Rahoton ya ƙara da cewa, ana fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a yankin Arewa maso Gabas, musamman a Borno ta tsakiya, da Arewacin Yobe, da kuma wasu sassan Gabashin Sakkwato.
ƙananan hukumomin da abin ya shafa a Arewacin Borno sun haɗa da Mobbae da Ngarcail, da kuma Mashi dake Arewacin Katsina.
Muhimman abubuwan da ke haifar da matsalar ƙarancin abinci, kamar yadda bincike na CH ya nuna, sun haɗa da rikici da rashin tsaro, kamar tada ƙayar baya, da yin fashi da makami, da kuma garkuwa da mutane, da kuma babbar matsalar da ke taƙaita gidaje na tunkarar tashin hankali.
Sauran abubuwan sun haɗa da tsadar abinci, rage yawan kayan abinci a matakin gida, ƙarancin ayyukan samar da kuɗin shiga, rashin isasshen abinci, da ƙarancin ruwan sha da tsaftar muhalli.
Wakilin FAO, Koffy Dominique, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da masu ruwa da tsaki na CH na ƙasa saboda nasarar kammala zagaye na tsawon makonni biyu na watan Fabrairu- Maris 2025 CH, wanda aka fara a hukumance a ranar 20 ga Fabrairu a cikin jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya.
Ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru biyu da suka wuce, ƙasar nan ta samu hauhawar farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru sama da 20, wanda ya jefa gidaje da dama cikin halin ƙunci na tattalin arziki, lamarin da ya sa suke da wahala wajen samun abinci da sauran kayayyakin masarufi.
Ya kuma ƙara da cewa, ƙasar ta kuma ga irin mummunan tasirin da matsanancin yanayi ke haifarwa, musamman ma ambaliyar ruwa, da kuma rikice-rikicen makami da miyagun laifuka, waɗanda ke haifar da rashin tsaro na tsawon lokaci, lamarin da ke ƙara taɓarɓarewar matsalar ƙarancin abinci.
Dominique ya bayyana cewa, babban maƙasudin taron nazarin binciken na CH, wanda ake gudanarwa sau biyu a shekara, shi ne tattara yawan jama’a da yankunan da ke fuskantar barazanar ƙarancin abinci da abinci mai gina jiki a ƙasar. Ya yi nuni da cewa, hukumar ta CH ta kuma ba da shawarar matakan da suka dace don hana afkuwar gaggawa ko kuma ta’azzarar matsalar abinci.