‘Yan Nijeriya na cigaba da nuna ɓacin rai a kafafen sada zumunta dalilin wani mutumin-mutumi na zinare na matar shugaban ƙasa Remi Tinubu da Ooni na Ife ya gabatar.
Hakan ya faru ne a wani biki a cikin jami’ar Obafemi Owolowo a lokacin da Oba Adeyeye ke gabatar da wasu ƙere-ƙere ga manyan baƙi da su ka halarci bikin.
Oonin ya haɗa da sanya wa wani titi mai tsawon kilomita 2.7 a cikin jami’ar da sunan matar shugaban ƙasar.
Ya bayyana matar shugaban ƙasar a matsayin wadda ta kasance mai taimakawa al’umma da kuma haɗin kan ƙasa.
Da wannan ne ‘yan Nijeriya da dama suka nuna rashin jin daɗin su kan wannan almubazzaranci yayin da mutane ke fama da ƙunci da matsin rayuwa.