Myanmar: An maka Suu Kyi a kotu

Daga FATUHU MUSTAPHA

Rahotanni daga ƙasar Myanmar sun tabbatar da cewa an gurfanar da jagorar Myanmar, Aung San Suu Kyi gaban kotu a Larabar da t gabata, kwanaki biyu bayan tsare ta da sojojin da suka kifar da gwamnatin ƙasar suka yi.

Kazalika, bayanai sun ce, kiraye-kirayen tada ƙayar baya don nuna adawa da juyin mulkin ƙasar sai ƙaruwa suke.

Ƙasar Myanmar da ke Kudu maso gabashin nahiyar Asiya ta sake faɗawa cikin mulkin soji ne bayan da wasu gungun sojoji suka damƙe jagororin mulkin farar hula a Litinin da ta gabata, lamarin da ya kawo ƙarshen mulkin dimokraɗiyyar ƙasar da bai shafe wasu shekaru masu yawa ba.

Ba a sake ganin Suu Kyi a bainar jama’a ba tun bayan da jam’iyyarta ta National League for Demoracy, NLD, ta samu gagarumar nasara a zaɓen Nuwamban 2020. Amma sojojin ƙasar, waɗanda jam’iyyarsu ta sha mummunan kaye suka ayyana zaɓen a matsayin mai cike da maguɗi.

Kakakin jam’iyyar NLD, ta sanar da gurfanar da Suu Kyi ‘yar shekara 75 a gaban kotu, a kan abin da ya shafi zargin saba wa dokar fita da shiga da kayayyaki, amma kotu ta ɗage sauraron ƙarar har sai nan da makonni biyu.

Tuhumar da ake yi wa jagorar Myanmar ɗin ta samo asali ne daga binciken da aka yi a gidanta biyo bayan kame ta, inda aka gano na’urorin tafi–da–gidanka na walkie-talkies, kamar yadda takardun tuhumar ‘yan sanda da suka shiga hannun manema labarai suka nuna.

Idan dai za a iya tunawa, ko a farkon wannan makon, Jaridar Manhaja ta ruwaito yadda magoya bayan Suu Kyi suka yi gangami tare da buƙatar a saki shugabanninsu da aka tsare.