Myanmar: An yi arangama tsakanin magoya bayan sojoji da ɓangaren Suu Kyi

Rahotanni daga Ƙasar Myanmar sun nuna cewa, magoya bayan sojin da suka yi juyin mulki a ƙasar sun yi arangama da masu adawa da kifar da gwamnatin Aung San Suu Kyi a birnin Yangon, yayin da hukumomi suka daƙile ɗalibai a makarantunsu don hana su zanga-zanga.

Tun lokacin da sojoji suka yi juyin mulki a ranar 1 ga Fabairu, tare da tsare Suu Kyi, ƙasar ta tsunduma cikin tashin hankali.

Kimanin makonni uku kenan da ake gudanar da zanga-zanga a kowacce rana da kuma yajin aiki a ƙasar.

Sai dai ‘yan sanda sun rufe ƙofofin makarantun da nufin hana ɗarruruwan ɗalibai fita.

Duk da cewa, an hana ɗaliban fita, amma an samu hatsaniya tsakanin magoya bayan sojoji da kuma magoya bayan Suu Kyi, inda rahotanni ke cewa wasu sun ji raunuka

Bayanai sun tabbatar da cewa magoya bayan sojojin da adadinsu ya kai dubu ɗaya sun yi barazana hatta ga ‘yan jarida da masu ɗaukar hoto, yayin da suka yi ta barbe-harbe da duwatsu.