Myanmar: Magoya baya sun buƙaci a sako Suu Kyi da sauransu

Daga WAKILIN MU

‘Yan jam’iyyar National League for Democracy a ƙasar Myanmar, sun yi kira da a sako Aung San Suu Kyi tare da sauran jagororinsu da aka tsare a Talatar da ta gabata. Suna masu bayyana juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi a ƙasar a matsayin al’amari da ya yi wa tarihin sojin ƙasar tabo mara kyau.

Da sanyin safiyar Litinin da ta gabata sojoji suka kama Suu Kyi da ta kasance shugabar jam’iyyarsu tare da shugaban ƙasar, Win Myint.

Bayan juyin mulkin, ba tare da ɓata lokaci ba sojojin suka naɗa wani tsohon janar, Min Aung Hlaing, a matsayin shugaban ƙasar tare da miƙa masa duka madafun ikon gwamnati.

Da wannan, ƙasar ta koma tsarin mulkin soja kenan bayan da ta shafe shekaru goma kacal a kan turbar dimokuraɗiyya.

Kawo yanzu dai babu wani bayani a hukumance game da inda Suu Kyi take tun bayan da aka dauke ta. Sai dai wata majiyar jam’iyyarsu ta shaida wa manema labarai cewa, suna da yakinin ana tsare da ita a Naypyidaw, babban birnin ƙasar.

Kazalika, baya ga buƙatar a sako musu shugabanninsu, ‘ya’yan jam’iyyar sun buƙaci sojoji su tabbatar da sakamakon babban zaɓen 2020 da ya gudana a ƙasar.