Naɗa Farouk Kurawa muƙami cigaba ne ga Jihar Kano – Ƙungiya

An bayyana naɗe-naɗen da Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf ya yi na PPS Dr. Farouk Kurawa a matsayin babban cigaba ga Jihar Kano da al’ummarta.

Shugaban ƙungiyar Youth Solidarity Forum a Jihar Kano, Comrade Dahiru Muhammad Maihula ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai da yammacin ranar Lahadin da ta gabata a sakatariyar ƙungiyar

Muhammad ya Bayyana Dr. Farouk Kurawa a matsayin haziƙi kuma fasihi wanda ƙwarya ce aka sakata a gurbinta.

Tun da fari, Shugaban ƙungiyar ya yi fatan alheri da addu’ar cimma nasara ga Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Comrade Aminu Abdulsalam Gwarzo wanda suka sha rantsuwar kama aiki a Litinin, 29 ga watan Mayu, 2023.

Kazalika, ya yi amfani da wannan fama wajen taya murna a madadin mambobin Ƙungiyar Kano Youth Solidarity Forum ga duka zaɓaɓɓun sanatoci da da ‘yan majalisar wakilai da na jiha murnar nasarar lashe zaɓe a matakai daban-daban.

Haka kuma Ƙungiyar ta taya waɗanda sabbin naɗe-naɗen ya shafa murna kama daga Sakataren Gwamnantin Jihar Kano, Sanata Dr. Baffa Bichi, Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Hon. Dr. Shehu Wada Sagagi, Dr. Farouk Kurawa PPS a matsayin Babban Sakatare na Musammam a Fadar Gwamnatin Jihar Kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, Chief Protocol, Hon. Sanusi Bature Dawakin Tofa, sakataren yaɗa labarai a fadar Gwamnatin Jihar Kano da sauransu.

Daga ƙarshe, Shugaban ƙungiyar ya jaddada godiyarsu dangane da nad’ɗin da Engr. Abba Kabir Yusuf yayi na Dr. Farouk Kurawa wato PPS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *