Naɗa Owoade a matsayin Alafin ya saɓa wa doka – Masu zaɓen sarki ga Gwamnan Oyo

Daga BELLO A. BABAJI

Amincewa da naɗin Frins Abimbola Owoade a matsayin sabon Alafin ɗin Oyo ya fusata masu zaɓen sarki da Gwamna Seyi Makinde na jihar ya yi a Masarauta mai daɗaɗɗiyar tarihi ta Oyomesi.

A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa Labarai da Wayar da kai na jihar, Frins Dotun Oyelade ya fitar, gwamnan ya amince da naɗa Owoade a matsayin Alafin ɗin bayan nazari da gabatar da shi da Oyomesi suka yi.

Haka ma Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu, Hon Ademola Ojo ya ce sanarwar ta rufe duk wasu batutuwa na al’umma ko ƙa’idodin shari’a da aka tayar da su tun bayan mutuwar tsohon Alafin, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III April 22, 2022.

A wata takarda da aka aika wa gwamnan, tawagar masu zaɓen sarkin ta bayyana naɗin Owoade a matsayin saɓa wa doka, ta na mai cewa ba ta amince ba saboda ba ta aika da sunansa ga gwamnan ba.

Majalisar ta tabbatar da cewa wanda ta miƙa sunansa ga muƙamin kaɗai shi ne Frins Lukman Gbadejesin bayan mafi yawancin mambobin tawagar sun zaɓe shi.

Haka kuma tawagar ta yi kira ga gwamnan da ya martaba ƙa’idodin da aka shar’anta wajen naɗa Sarkin.