Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kwamandan Operation Haɗin Kai, Manjo Janar Ibrahim Ali, ya ce sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok, Saratu Dauda, wadda ta bar ‘ya’yanta uku tare da ‘yan ta’adda a dajin Sambisa da ke jihar Borno.
Hakan ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu abokan karatunta guda biyu Esther Marcus da Hauwa Maltha, sun tsere, inda sojojin Nijeriya suka same su tare da kai su ga gwamnatin jihar Borno.
Ali, yayin da yake miƙa Saratu ga kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Borno, Zuwaira Gambo, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, ta ce sojoji sun cetota ne a wani samame da suka yi a yankin Ukuba, a dajin Sambisa.
Ya ce Saratu, mai shekaru 25, wacce ke kan lamba 10 a jerin ‘yan matan makarantar Chibok da aka sace, ‘yar asalin Umbula ce, a Qaramar Hukumar Chibok ta jihar Borno.
“Ta tava auren wani Abu Yusuf, wanda daga baya suka rabu, kafin ta auri Baana, wanda aka fi sani da Abu.., dukkansu ‘yan ta’addan Boko Haram ne.
“Saratu tana da ‘ya’ya mata uku; ta bar su a mavoyar ‘yan ta’addar. Ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da ƙoƙarin ceto ‘ya’yanta da sauran mata da ƙananan yara.
“A cikin kwanaki 10 da suka gabata Saratu ta yi jinya a ɗakin taro na 7 Div. Asibitin lafiya da ke Maimalari Cantonment kuma a yau za mu miqa ta ga jami’an gwamnatin jihar Borno daga ma’aikatar mata a hukumance.
“Ya zuwa yau, alƙaluman ‘yan matan makarantar Chibok 276 da aka sace sun nuna cewa ‘yan mata 57 ne suka tsere a shekarar 2014, an sako ‘yan mata 107 a shekarar 2018, an ƙwato uku a shekarar 2019, an ƙwato biyu a shekarar 2021, an ceto 11 a shekarar 2022, sannan an ceto uku zuwa yanzu a 2023, “inji shi.
Ali ya ce adadin ‘yan matan Chibok 183 da aka yi garkuwa da su ne, yayin da ‘yan matan 93 ba a gansu ba.
A cikin hirarta da manema labarai, Saratu ta ce, “Na tuntuɓi mijina na tambaye shi ko zai iya ba ni damar in je wurin iyayena in yaye musu duk wata damuwa da suke damunsu amma ya ce Saratu, ba zan iya yanke shawara kan hakan ba. Kun san halin da muke ciki, kuma wannan zai jefa ni cikin matsala.
“Na kuma roƙe shi cewa, idan zan tafi, zai bar ni in tafi da ‘ya’yana uku amma ya ki, don haka nace ba zan bar yarona ba ko da menene domin ba zai samu sauƙi ba in rayu ba tare da ita ba, wanda ya wajabta.
“Bayan wani lokaci, wani waliyin da aka ba mu amana lokacin da muka isa dajin Sambisa, Malam Ahmad, ya zo ya shaida min cewa yana sane da shirina na tserewa. Ya ba ni shawarar kada in yi haka, kuma idan akwai wani abu da nake buƙata, zai taimake ni da shi.
“Bayan na fahimci hakan, na ɓoye shirina kuma na tabbatar masa cewa zan bi maganarsa. Daga baya, na gaya wa mijina cewa ba zan ja da baya ba. Na bar yaran a ɗakinsa na tsere daga tarkon maharan,” inji ta.