Na fuskanci ƙalubale a neman ilimin boko – Hon. Hafsat Abdullahi

“Da kaina na yi fafutukar samun ilimin boko”

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Honorabul Hafsat Abdullahi cikakkiyar ‘yar siyasa ce da ta riqe muƙaman siyasa daban daban a Jihar Nasarawa. A yanzu ita ce mataimakiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya kuma hedikwatar gwamnatin jihar. A tattaunawarta da wakilinmu, ta bayyana tarihin rayuwarta da ƙalubale da ta fuskanta a rayuwa da sauransu, inda ta kuma shawarci ‘yan uwanta mata su yi dukka mai yuwa wajen neman ilimin zamani da na addini da sauransu. Ga yadda hirar ta kasance:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.
HONORABUL HAFSAT: Sunana Honorabul Hafsat Abdullahi. An haife ni a garin B.A.D dake yankin Ƙaramar Hukumar Lafiya anan Jihar Nasarawa. Na fara karatun firamare ɗina a garin B.A.D. Daganan na ci gaba da karatun sakandare ɗina a nan B.A.D inda na kammala a John Bosco College dake garin Doma hedikwatar Ƙaramar Hukumar Doma a jihar nan. Daganan na ci gaba a wani babbar makarantar Islamiya dake nan garin Lafiya inda na samu certificate na grade 2 ɗina. Bayan na kammala ne sai na ci gaba a babbar jami’ar tarayya dake nan garin Lafiya inda na kammala karatun babbar difuloma ɗina a fannin shugabanci wato ‘public Administration’ kenan a turance.

Bayan karatu, ko kin fara aiki ne?
Na fara aiki ne anan sakatariyar Ƙaramar Hukumar Lafiya kafin daga bisani na shiga siyasa ana dama wa da ni. Kuma kamar yadda ka sani daga cikin muƙaman siyasa da dama da na rike akwai na baya bayan nan wanda maigirma gwamnan jihar nan Umaru Tanko Almakura ya bani na mataimakiyarsa ta musamman akan harkokin hulɗa da jama’a. Kamar yadda ka sani muƙamin da na riƙe kenan har aka zo lokacin zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar nan, inda na fito takarar a matsayin muƙaddashiyar shugaban Ƙaramar Hukumar Lafiya na yanzu inda da yardar Allah kuma muka yi nasara. Matsayi da nake riƙe da shi kenan kawo yanzu kamar yadda ka sani.

Bari mu koma ɓangaren tasowarki. Me kika koya a zamanki da iyayenki?
A gaskiya iyayena musamman mahaifina ya koya min halaye nagari da nake matuƙan cin moriyarsu a rayuwata a yau. Kuma babban abinda ya koyamin shi ne, yadda zan zauna lafiya da maƙwabta da sauran alumma da nake cuɗanya da su. Kasancewa mahaifina mutum ne dake matuƙar son zaman lafiya har ana masa iƙirari da alƙalin gida. Don ya kasance har kotu yake zuwa ya karɓi magana ya zo gida ya sasanta waɗanda ke riciki. 

Saboda haka, kodashike mahaifina ya kasance mutum ne wanda bai ɗauke neman ilimin boko dina da mahimmanci ba a lokacin amma zan iya cewa na ci gagarumar moriyar tarbiyyarsa a rayuwana musamnan a ɓangaren zamantakewa irin na zaman lafiya. Kai bani kaɗai ba har da sauran ‘yan uwa da makwabta duk sun ƙaru da kyawawan halayensa. Kuma kamar yadda ka sani zaman lafiya shine babban abu a rayuwar nan da muke ciki. Don idan babu shi babu abinda mutum zai iya yi komai ilimi da yawar dukiyarsa. Shiyasa mahaifina yafi ba da fifiko a ɓangaren. Saboda haka a taƙaice zance Allah ya ci gaba da saka wa iyayena da alheri dangane da wannan kyakkyawar tarbiyya da suka koya min da sauran ‘yan uwana bakiɗaya da muke tasowa.

Wane buri kike da shi?
A gaskiya da nake ƙarama, na so ne na zama likita. Don na so ne ace ni ma ina ba da tawa gudunmawa a ɓangaren kare lafiyar al’umma bakiɗaya. Don kamar yadda ka sani lafiya ita ce uwa uba idan babu ta sai a hankali. Kuma a duk lokacin da na ziyarci asibiti ko wasu wuraren samar da magunguna nakan Matuƙar tausayawa hali da marasa lafiya ke ciki. Don za ka ga galibinsu basa iya komai sai dai a yi musu. Shiyasa naso a lokacin ace nima ina tallafa musu. Amma a rayuwa kana naka Allah yana nasa. Kuma idan Allah bai nufe ka da yin wani abu ba, abin ba zai taɓa yi wa ba, duk yadda ka yi. 

Sai dai duk da haka, a yau ina matuƙar godiya ga Allah da yake amfani dani a wani hanyan daban wajen bauta wa al’ummata dai-dai gwargwado. Don aiki da muke yi kenan anan sakatariyar ƙaramar hukumarmu ta Lafiya da jihar nan bakiɗaya. 

Muna tabbatar da aiwatar da kyawawan manufofi da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin maigirma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da na jihar nan ƙarkashin jagorancin Umaru Tanko Almakura ne wa ɗimbin al’ummarmu bakiɗaya musamman Waɗanda ke yankunan karkara. Saboda haka kodashike ban cimma burin zama likitar ba alhammdu llillah a yau.

Rayuwa na tattare da ƙalubale. Ko kin fuskanci ƙalubale a tafiyarki?
A gaskiya ba zan taɓa manta babban ƙalubalen da na fuskanta a lokacin da nake tasowa shi ne, a ɓangaren neman ilimin boko ɗina. Kamar yadda na bayyana maka a baya iyayena sun kasance mutane ne da ba su ɗauki harkar ilimina da mahimmanci ba, da nake tasowa. Waɗannan karatu dana bayyana maka cewa na yi nan ma da kaina na yi ta fafata wa, da yake ina da ra’ayin karatun har Allah ya taimake ni na kammala. Shi ya sa ma ban gaya masu ba. 

Saboda kawai ba sa buƙatana da karatun, suka sa na yi aure tun ina makarantar sakandare inda ina karatu ina kuma da aure kafin daga bisani muka rabu da mijina. Saboda haka wannan shi ne nake gani a matsayin babban ƙalubale dana fuskanta a rayuwana bakiɗaya. Don da na samu ƙarfafawa a ɓangaren tun farkon rayuwana da a yanzu na yi nisa fiye da yadda nake yanzu a karatuna. Amma duk da haka alhammdu llilah don na tunkari ƙalubalen na kuma na ce na ci gaba a ƙoƙarin kaina da taimakon Allah har na kammala karatun kuma ga shi a yau ina cin moriyarsa.

Mu ji nasarorin da kika samu?
A gaskiya ba yabon kai ko alfahari ba idan batun samun nasarorin rayuwa ne sai dai in ce alhamdu llillah. Don ni Allah ya yi ni da wani baiwa ce ta musamman, inda na kasance mace da duk abinda ta sa a gaba sai ta yi nasara. Na samu nasarori da dama da lokaci bazai bani dama in bayyana maka ɗaya bayan ɗaya ba. Kuma har yanzu ina ci gaba da samunsu. 

Waɗannan muƙaman siyasa da ayuka da na bayyana maka cewa na yi kuma ina yi har yanzu dukkansu nasarori ne da Allah ya bani a rayuwa. Don ai akwai wasu da dama da sun ma fini basira da ilimi da sauransu, amma ba su samu wannan dama dana samu ba. Kuma idan baka sani ba, inaso in sanar da kai cewa, ba a taɓa yin mace mataimakiyar shugaban ƙaramar hukuma ba a faɗin jihar nan bakiɗaya ba sai a kaina. Kaga shi ma kawai ba ƙaramar nasara ba ne a rayuwata. Don ina yin amfani da dukka waɗannan dama ne wajen bada tawa gudunmawa wajen cigaban al’ummata bakiɗaya dai dai gwargwado a kulli yomin.

Honarabul Hafsat a wajen taron siyasa

Saboda haka a gaskiya idan batun nasarori ne na samesu da dama a rayuwana kuma jama’a da nake bauta musu ne zasu fi bada shedar. Kuma ina gode wa Allah dake tare da ni a kowanne lokaci yana kuma tabbatar min da alherinsa a duk abinda na tunkara a rayuwa don ba yin kaina ba ne, yin sa ne da baiwarsa.

Ko akwai wani abu da za ki so a tuna ki da shi?
To ni dai a gaskiya zan so a tuna dani a matsayin mace da ta yi dukka mai yiwuwa wajen taimakon al’ummarta. Don abinda nake yi kenan. Kaga Allah ya yi ni mace ce da ba ta damu da tara dukiya ba. Wannan ba shi ne damuwa ta a rayuwa ba. Allah ya yi ni mace ce mai wadatar zuci. Duk abinda Allah ya ba ni ina godiya in kuma raba shi da al’ummata. Tsarin rayuwata kenan. Kuma ina samun albarkar Allah ta wannan abu da nake yi. Saboda haka abinda zan so a tuna da ni bayan na bar duniyar nan shi ne mace da ta yi tafiya da kowa ta kuma tallafa wa al’ummarta dai-dai gwargwado da take raye.

Wace shawara za ki ba wa mata ‘yan uwananki?
A kullum shawarar da nake bai wa mata ‘yan uwana bakiɗaya musamman wadanda ke tasowa shi ne, a yayin da suke neman ilimin addini su haɗa dana zamani. Don zamani ya canja dole sai da ilimi mace za ta iya bada tata gudunmawar a rayuwanmu a yau. Dukka waɗannan nasarori da na bayyana maka na samu a rayuwa galibinsu suna da alaƙa ne da karatu. 

Saboda haka an kai wani lokaci ne a rayuwan nan da dole mace ta nemi ilimi ko ta kama sana’a. Maganar gaskiyar kenan. Idan mace ba za ta iya neman ilimi ba, to ta tabbatar ta kama sana’a tana yi komai ƙanƙantar ta. Don ta haka ne kawai za ta iya tsare mutuncinta da na iyalanta ta kuma samu damar taimaka wa al’ummarta bakiɗaya a ɓangaren da ta ƙware. 

Mu na godiya.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *