Na gama haddace halayen Buhari don zama Shugaban Ƙasa – Osinbajo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Farfesa Yemi Osinbanjo ya ce ya naƙalci duk wasu halaye na Shugaba Muhammadu Buhari, inda ya ce hakan zai taimaka masa wajen zama Shugaban Ƙasa.

Osinbanjo ya furta hakan ne ranar Juma’a yayin wata ganawa da ya yi da wakilan Jam’iyyar APC a Jihar Oyo.

Da yake bayyana nagartar sa a gaban wakilan, mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya share shekaru dama yana samun horo da kuma shirye-shirye.

Osinbanjo ya yi amannar cewa yana da ƙwarewar da zai tafiyar da ƙasar nan matuƙar ya gaji kujerar Shugaba Buhari a zaɓen 2023 mai zuwa.

Kwanan nan dai Farfesa Osinbanjo da tawagarsa suka kai wa Olu na Ibadan, Sanata Lekan Balogun ziyara gidansa domin bayyana masa aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *