Na horar da masu ƙananan sana’o’i 4,000 fasahar kasuwancin yanar gizo – Maryam Bichi

“Samun mata a cikin harkokin kasuwanci zai ƙara zaman lafiya da yalwatar arziƙi”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Harkar kasuwanci ta kafafen sadarwa na zamani ba sabon al’amari ba ne a ƙasar nan, musamman ma a wajen matasa waɗanda a lokacin su ne wannan cigaba yake daɗa samuwa. Sai dai ta yaya mutum zai samu ilimin yin wannan harka, da kuma kaucewa faɗawa hannun miyagu masu damfarar jama’a. Wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu ya zanta da wata matashiya daga Jihar Kano, wacce ta yi fice a kan wannan irin kasuwanci na zamani da ta ce ta koyar da matasa da masu ƙananan sana’o’i fiye da dubu huɗu yadda za su inganta sana’o’in su, ta kuma bayyana masa yadda wannan harka ta inganta rayuwar ta har ta zama abin koyi ga wasu. A sha karatu lafiya.

MANHAJA : Mu fara da jin cikakken sunanki da abin da ki ke yi a rayuwa.

Sunana Maryam Abbas Abdulkadir Bichi, amma an fi kirana da Maryam Bichi. Ni ýar kasuwa ce mai amfani da hanyoyin sadarwar zamani don tallata haja ta da ta sauran jama’a, wato abin da ake kira a turanci da Digital Marketer. Ina kuma bada shawara da koyar da masu buƙatar samun ilimi kan duk ɓangaren da ya shafi kasuwancin kaffen Sada Zumunta wato Social Marketing. Ni ce shugabar kamfanin dillancin kayayyakin ado na mata a yanar gizo na Easysmart Online. Kuma yanzu haka ni ma’aikaciya ce a kamfanin sarrafa madarar shanu ta L & Z da ke Kano.

Ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwar ki.

An haife ni a ranar 26 ga watan Yuni a shekarar 1994. Na fara karatuna a makarantar rainon yara ta Childs Foundation da ke Legas, da makarantar New Capital School Asokoro a Abuja. Na kammala karatuna na firamare a makarantar Ma’aikatan Kwalejin Tarayya ta ‘Yan Mata da ke Kano wato FGC Staff School, Kano. Na yi karatun sakandire da Saukar Al’ƙur’ani a makarantar mata ta Kano Foundation Girls Secondary School Bebeji a Shekarar 2010. Sannan na yi Diploma avangaren ilimin fasahar zamani a HiiT, a shekarar 2010. Daga nan na shiga Makarantar Share Fage don neman shiga jami’a ta College of Arts Science and Remedial Studies Kano, wacce aka fi sani da CAS, inda na yi IJMB a ɓangaren kimiyya a 2011.

Na shiga makarantar Koyon Sana’o’i ta Adults Health & Information Project (Ahip) da ke hanyar Maiduguri a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2012, inda na koyi sana’ar ɗinki da sana’ar hannu. Na samu damar yin karatun digirina na farko a fannin nazarin kimiyyar sanin ƙasa a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil a nan Kano tsakanin shekarar 2012 zuwa 2016.

Sannan na yi aikin Hidimar ƙasa (NYSC) a Jihar Jigawa. Yanzu haka kuma ina cigaba da karatun digirina na biyu a fannin sana’o’i a Makarantar Koyar da Harkokin Kasuwanci ta Ɗangote da ke Jami’ar Bayero ta Kano

Nayi ayyuka da dan dama da wasu kungiyoyi da kuma kamfanoni a matsayin mai tsara tallace-tallace ta kafofin sadarwa, ina da shaidar ƙwarewa ta musamman kan tallace-tallacen kafofin sadarwa na zamani, wanda kamfanin Facebook Nigeria ta ba ni.
Bugu da qarin kuma ina da kamfanina na kaina da muka kafa shekaru 6 da suka gabata, wato Easysmart Concept inda muke sana’ar sayar da kayan ado na mata irin su sarƙoƙi da ýan kunne, wanda yanzu ya sauya zuwa kamfanin tallace-tallace ta yanar gizo wato Easysmart Online.

Wanne abu ne za a iya cewa Maryam Bichi ta fi shahara a kansa?

A gaskiya a duk tsawon rayuwata abubuwan da na fi yi duk sun shafi harkokin kasuwancin zamani ne ko kuma a ce kasuwancin yanar gizo wato Digital Marketing.

Kina daga cikin matasan mata da ke ƙoƙari wajen harkokin kasuwanci ta yanar gizo, menene ya ja hankalinki ga wannan ɓangare?


Gaskiya ne, yanzu a garin Kano da Arewa bakiɗaya ina daga cikin mutane masu wayarwa da matasa kai a kan abin ya shafi kasuwancin yanar gizo, da yadda mutum zai inganta sana’ar sa.

Abin ya jawo hankali na shi ne, ganin yadda matasan mu suke koma baya a fannin fasaha da kuma ƙwarewa a wannan ɓangaren shi ya sa na ɗau aniyar koyarwa da wayar da kan mutanen mu domin mu amfana da abin da zamani ya zo da shi. Don haka ne ma akasari na fi yin ayyukana da suka shafi koyarwa da ba da horo da harshen Hausa.

Yaya ki ke ganin tasirin kafafen sadarwa ga cigaban harkokin cinikayya da kasuwanci?

Gudanar al’amura na yau da kullum kamar karatu, neman labarai, da rahotanni, sadar da zumunta da abokai da ‘yan uwa, a kan yanar gizo ya sa dole mutane da yawa su dogara da harkokin sada zumunta na intanet don neman samfur an abubuwan da ake sarrafawa ko sana’antawa, da irin ayyukan da suke buƙata. A cikin kaso ɗari na mutanen duniya kaso Sittin suna amfani da yanar gizo. Don Haka duk wani ɗan kasuwa wanda ba ya amfani da waɗannan shafuka yadda ya kamata yana fuskantar haɗarin rasa damar samun ciniki a wannan zamani.

Ka ga kenan kafafen sadarwa na zamani suna da tasiri babba wajen cinikayya da saye da sayarwa, saboda mutane bila-adadin suna hawa kafafe daban daban.

Matasan mata da dama a Nijeriya sun shiga irin wannan harkar kasuwanci ta zamani, kina ganin mai ya kawo wannan canji?

Ba wani abu ba ne kamar yadda na faɗa a baya, canji ne ya zo wa duniya kuma jama’a da dama sun raja’a a kan kafafen sadarwa na zamani a kusan komai yanzu, don haka kasuwanci ta yanar gizo na daga cikin abubuwan da suka fi samun karvuwa sosai a duk duniya.

Ba a jima ba da ki ka gudanar da wani bikin Mu Inganta Sana’ar Mu, a birnin Kano, ba mu labarin wannan salon kasuwancin?

Shi Taron Mu Ingata Sana’ar mu taro ne na ƙarawa juna sani wanda za a haɗu a tattauna matsalolin da suka shafi kasuwanci, sana’o’i da sauransu, kuma duk shekara muke shiryawa. Ƙudirin taron ya ƙunshi inganta kasuwanci ta hanyar fasahar zamani wato Technology & Digital Marketing. Ana gayyato masana da ƙwararru a bangaren matakan cigaban rayuwa, fasahar zamani da kasuwanci, don su ƙara wayar mana da kai. Salo ne na haɗuwa da juna tsakanin abokan hular kasuwanci don faɗaɗawa da kuma tallata kai.

Wacce nasara za ki iya cewa, wannan taron naku ya samu?

Taron Mu Inganta sana’armu ya samu karɓuwa sosai, kuma daga cikin nasarorin da aka samu sun hafa har da samun haɗuwar mutane kusan 350 da suka samu damar halarta. Sannan akwai ƙananan ‘yan kasuwa (wato SME’S) guda 50 ne suka baje kolin kayansu, kuma duk sun yi ciniki kamar yadda wasun su suka bayyana, har da masu cinikin sama da dubu ɗari. Sannan an yi ƙara haɗa gwiwa da ɓangarori daban daban na ýan kasuwa, domin kara ilimantar da juna, wanda ya sa mutane suke ta roƙon mu da mu cigaba.

Menene burinki nan gaba a wannan ɓangaren kasuwanci da ki ke yi?

Burina nan gaba shi ne na buɗe babban kamfani ko masana’anta da ke ƙunshe da makarantar koyar da kasuwancin kafafen sada zumunta, da samar da babbar manhajar saye da sayarwa da za ta tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa.

Yaya ki ke ganin za a kawar da ƙalubalen ýan damfara a wannan harkar kasuwanci ta zamani?

A nawa ganin ya kamata, mutane su zama masu riƙe amana da gaskiya a duk abin da zasu yi a kan yanar gizo. Sannan mutane su koyi yadda za su samar da tsaro da kariya ga shafukansu ta hanyar saka Two-way Aunthentication da kuma sannin irin shafukan da za su riƙa dannnawa, ko za ka yi cinikayya da shi.

Wacce shawara za ki bai wa sauran mata da matasa game da wannan harka?

Ina bai wa mata da maza ‘yan uwana da su riƙe harkar kasuwancin zamani da mahimmanci, saboda yanzu ita ce take samun karvuwa, su buɗe zukatansu da ƙwaƙwalensu su koyi abin da ya shafi fasaha da kuma neman ilimi a kai.

Wanne alheri za ki iya cewa kin samu ta dalilin wannan kasuwanci na zamani da ki ke yi?

Alhamdu lillahi, na samu nasarori masu yawa da ba za su ƙirgu ba. Babban abin alfaharin shi ne yadda nake kula da kaina da duk wasu buƙatuna, tare kulawa da ‘yan uwana, wannan yana daga cikin babbar nasarata. Sannan yadda nake ƙarfafa gwiwar mutane da tasirin da na yi a rayuwar wasu da suke kallona kamar wani madubi, na zama abin koyi a wajensu. Ban da tallafi wato grants da na tava samu har sau biyu, da sanin mutane manya a harkar cinikayyar zamani da kuma samun damar shiga hira da manyan kafafen watsa labarai na ƙasa da duniya irin su Arewa24, BBC, NTA, Zamani TV, Tozali, Liberty da sauransu. Sannan har wa yau a tsukin shekara huɗu da na fara zuwa yau na horar da matasa da ƙananan ‘yan kasuwa da yawan su ya kai 4,000 daga yanar gizo zuwa aji na na zahiri.

Wanne tasiri ki ke ganin an samu dangane da koyarwar da ki ke yi wa masu ƙananan sana’o’i a wannan harka?

Alhamdu lillahi, kamar yadda na faɗa a baya tun daga aikina da kamfanin facebook a shekarar 2019 na fara horarwa zuwa yanzu, na koyar da mata da matasa kusan 4 000, wanda cikinsu wasu sun fara kasuwancin kansu, wasu kuma suna wa wasu aiki, wasu sun yi amfani da ilimin sun bunƙasa sana’a’ion su.

Maryam

Wanne tallafi ki ke buƙata, in da za ki samu daga gwamnati, ƙungiyoyi, ko masu hannu da shuni, don bunƙasa harkokin ki?

Babban tallafin dai kamar yadda na bayyana mafarkina na gina babbar ma’aikata ta koyarwa bai wuce samun wadataccen jari ba, da kuma ƙarin tallata wa daga sauran al’umma.

Wacce rawa ki ke ganin mata za su iya takawa a harkokin kasuwanci da cinikayya a Arewacin Nijeriya?

Tabbas suna da babbar gudunmawa da suke takawa a bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa in har an ba su damar aiki, da kuma tallafin sana’a. Kuma suna masu ba da tarbiyya a cikin al’umma don samun mata a cikin harkokin kasuwanci zai ƙara zaman lafiya da yalwatar arziƙi.

Ban da kasuwanci, wanne abu ne yake ɗaukar hankalin ki, kuma ki ke sha’awar yin sa?

Bayan kasuwanci, kamar yadda na faɗa ina aiki da kamfanin sarrafa madara na L & Z Integrated Farms, a matsayin jami’ar kula da harkokin kasuwanci. Amma harkar da take burgeni da nake sha’awar shiga ita harkar watsa labarai da sadarwa.

Wacce shawara za ki bai wa masu ƙananan sana’o’in mu na Arewa, kan inganta harkokin su?

Shawarata ita ce su karɓi sabuwar fasahar zamani hannu bibbiyu, saboda akwai alheri a ciki. Sannan yana da kyau mutane su faɗaɗa tunanin su kuma su nemi ilimin abin da ba su sani ba.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Sannu sannu ba ta hana zuwa, sai dai a daɗe ba a je ba. Da kuma mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa!

Na gode.

Ni ce da godiya.