Na kashe ɗan acaɓa, na sayar da babur ɗinsa kan N310,000 – Wanda ake zargi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani da ake zargi da kisan kai, Abubakar Sadiƙ, ya amsa laifin yadda ya kashe wani ɗan acaɓa, ya kwace babur ɗinsa, ya sayar da shi kan N310,000 a jihar Neja.

Sadiƙ, a cewar ‘yan sandan, ya kashe Abdulrahman Isah ne, bayan ya hau babur ɗinsa daga unguwar Bosso da ke Minna zuwa Maitumbi.P.

Jami’in hulɗa da ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun ya bayyana cewa: “A ranar 02/01/2025 da misalin ƙarfe 2:00 na rana, an samu wata sanarwa cewa an gano wata gawa a unguwar Pyata-Maitumbi Bye-Pass na Bosso.”

Ya ƙara da cewa, jami’an ‘yan sanda na Bosso Diɓ sun je wurin da lamarin ya faru inda suka ga wata gawa ta wani mai suna Abdulrahman Isah mai shekaru 20 a ƙauyen Pyata cikin jini, wanda ake zargin an kashe shi ne an tafi da babur ɗinsa, yayin da aka kai gawar zuwa ɗakin ajiyar gawa na asibiti da ke kusa.

A ci gaba da gudanar da bincike, rundunar ‘yan sandan ta ce an kama wani Abubakar Sadiƙ da ke ƙauye da laifin faruwar lamarin kuma ya amsa laifinsa.

Ya ce wanda ake zargin ya bayyana cewa, “Na hau babur ne daga mahaɗar Berger, Bosso, zuwa Maitumbi. Yayin da muke kan hanyarmu, na yaudari ɗan acaɓar kuma na karkatar da shi ya bi hanyar da ba babu kowa a kan titin Pyata-Maitumbi Bye-Pass kuma na yi amfani da dutse na buga masa a kai.”

Ya ƙara da cewa, ɗan acaɓar ya sume, ya ɗauki babur ɗin ya tafi da shi. Daga baya ya kai kasuwar Beji, ya ba wani Ibrahim Garba mai shekaru 35 a ƙauyen Kuyi. Bosso ya sayar da shi akan kuɗi naira dubu ɗari uku da goma ga wani Bala Usman na Wushishi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an damƙe masu sayen kuma an kwato wasu kuɗi naira dubu ɗari uku.