Na kashe mutane sama da 20, cewar matashin ɗan ta’adda Naziru Sani

*Ana biya na tsakanin N20000 zuwa N30000 bayan kowane hari da muka kai – Sani

Daga BASHIR ISAH

Matashin nan ɗan shekara 21 da ake zargin ɗan ta’adda ne, wato Naziru Sani, wanda ke aiki a ƙarƙashin gawurtaccen ɗan ta’adda Bello Turji, ya yi iƙirarin cewa ya kashe sama da mutum 20 a hare-hare da dama a faɗin Nijeriya.

Matashin ɗan ta’addan ya bayyana hakan ne a lokacin da jami’i mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Gambo Isah, ya gabatar da shi a gaban manema labarai a babbar hedikwatar rundunar a ranar Talata.

An cafke Sani wanda mazaunin ƙauyen Maƙera ne, a yankin ƙaramar hukumar Tsafen jihar Zamfara kusa da Rukunin Gidajen Jabiri a ƙaramar hukumar Funtua, jihar Katsina bayan tattara wasu bayanan sirri, in ji SP Gambo.

A cewar matashin, “Tare da ni aka kai hare-hare a wurare da dama ƙarƙashin jagorancin ubangidana, Turji da ni mun kashe sama da mutum 20 a baya, amma yanzu na tuba.

Haka nan, ya ce, “Ni yaron Bello Turji ne, na yi aiki a ƙarƙashin umarninsa.”

Ya ƙara da cewa, “Tserewa na yi daga dajin Jangebe a jihar Zamfara inda Turji ke da ɓuya a yanzu yana fakon raina. ‘Yan sanda sun kama ni ne a Funtua a daidai lokacin da nake ƙoƙarin neman arcewa zuwa Suleja a jihar Neja, inda iyayena suke da zama.

“Na baro matata da ‘ya’yana a ƙauyen Maƙera da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.”

Da yake amsa tambayoyi, Sani ya ce suna da yawan gaske a ƙarƙashin Turji, tare da cewa, “Ana biya na tsakanin N20000 zuwa N30000 bayan kowane hari da muka kai.”

Bayanan ‘yan sanda sun ce an kai hare-hare masu yawa tare da matashin a sassan jihar Sakkwato da Zamfara tare da kashe jama’a da dama. Bincike dai na kan gudana, in ji ‘yan sandan.