Na rubuta littafin abinda ya faru da ni bayan fitowarsa – Zuwaira Kolo

“Har yau akwai waɗanda ba sa iya karatun littafi a waya”

Daga AISHA ASAS

Ɗaya daga cikin marubutan da suka jima su na ciyar da adabin Kano gaba ce Blueprint Manhaja ta ɗauko mu ku a wannan mako. Zuwaira Dauda Kolo marubuciya ce da ta jima ta na ƙawata zukatan makaranta da daɗaɗan littafai, masu fadakarwa gami da nishaɗantarwa kai har ma da ilimintarwa. A tattaunawarta da Wakiliyar Blueprint Manhaja, Aisha ASAS, mai karatu zai ji irin tata gwagwarmayar a duniyar rubutu. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Mu fara da jin taƙaitaccen tarihinki.
ZUWAIRA KOLO: Da farko sunana Zuwaira Dauda kolo. Ni Kanuri ce daga Jihar Borno a Ƙaramar Hukumar Shani. Jahar Filato ita ce jihar da aka haife ni, a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa. Nan aka haife ni, nan na yi karatuna tun daga matakin firamare har zuwa yau.

Wacce shekara ki ka fara rubutu?
Na fara rubutu 2006.

Zuwa yanzu littafinki nawa?
Littafai shida na rubuta, uku an buga, uku su na hanya, insha Allah.

Ko za mu iya jin sunayensu?
Waɗanda suka shiga kasuwa su ne; ‘Mardiyya’, ‘Bulalar Zuciya’, ‘Zubowar Hawayena’. Waɗanda ba su fito ba sune; ‘Marainiya’, ‘Azaba Kishin’ da ‘Faɗa Da Mahalicci’, sai ‘Na Gane Duniya’.

Mene ne dalilin da ya sa kika tsunduma harkar rubutu?
Na tsunduma harkar rubutu ne domin in faɗakar tare da wayar da kan al’umma, domin su qaru da baiwata, musamman mata.

A wane lokaci ki ka fi sha’awar yin rubutu?
Lokacin da na ke ni kaɗai, ko ina shiru, ko a bakin ruwa.

Shin kina fitar da littafai har yanzu ko kin ɗan dakata?
Eh to, tun shekaru huɗu baya na ɗan dakata. Amma kwanan nan ma zan fitar, insha Allah.

Wasu marubuta da ke buga litattafansu na canza sheƙa zuwa rubutu a yanar gizo, dalilin kasuwar ta su da ke neman ta kuɓuce masu. Shin kina ganin hakan ne mafita ga matsalar kasuwar littafan adabin Kano?
Canza sheka zuwa rubutu a yanar gizo ba shine mafita ba ga kasuwar littafan adabin Kano.

Ko akwai ƙungiyar da kike ciki ta marubuta?
Akwai ƙungiyoyin marubuta da dama da na ke ciki, daga fara rubutuna zuwa yanzu. Akwai Alƙalam Authors Kaduna, wadda ita ce farkon ƙungiyar da na fara shiga, akwai Mace Mutum. Akwai HAF, akwai Kainuwa da dai sauran su.

Me marubuci yake fatan masu a lokacin da ya shiga ƙungiyar marubuta?
Da farko tarba, yadda za a karɓe shi. Na biyu haɗin kai, fahimtar juna, riƙon gaskiya da amana.

Kenan ƙungiyoyin marubuta ana kafa su ne don kawai sada zumunta tsakanin marubuta?
Ana kafa su ne domin sada zumunta, ƙarfafa wa juna, musamman sabbin marubuta waɗanda za a dinga ƙarfafa su da kuma sakasu a hanya ta yadda za su dinga rubuta labari mai ma’ana, wanda idan duniya ta karanta, za ta amfana da kuma shawarwari da yadda za a samu cigaban adabi musamman sabbin marubuta na yanzu masu taso wa.

Shin ana iya gadon baiwar rubutu?
Eh, ƙwarai kuwa, ana iya gadon baiwar rubutu, musamman idan akwai shaƙuwa sosai tsakanin iyaye da ‘ya’yan.

Marubuta masu tasowa na ƙorafin ba sa samun taimakon manyan marubuta ire-iren ku, kuna wulaƙanta su a lokacin da suka nemi shawarwari a cewar su. Mene ne gaskiyar wannan maganar?
Wannan magana ba gaskiya ba ce. A iya sanina marubuci ba shi da wulaƙanci ko girman kai ko kaɗan, sai dai ya danganta da sigar da aka biyo mu su da shi. Yawancin marubuta masu tasowan wasu daga cikinsu ba su karɓar gyara da shawarwari daga tsofaffin marubuta. Don shi marubuci kullum burinshi a ce an samu cigaba. Kullum burin tsofaffin marubuta a ce sabbin marubuta masu tasowa sun samu ɗaukaka fiye da su. Misali; yanzu za ki ga Gasar marubuta da ake saka wa yawanci za ki ga ana ƙayyade shekaru, a ce kar shekarunka su wuce 35. Wannan wata dama ce da ake bai wa sabbin marubuta masu taso wa.

Ko akwai wani abu da ba za ki iya manta wa da shi a harkar rubutu?
Abinda ba zan taɓa manta wa ba shine; littafin na farko da na rubuta, ‘Mardiyya’, wanda na rubuta shi jarumin littafin ya yi hatsari a hanyar Saminaka, yana dawo wa daga Kaduna, ya samu karaya a ƙafa, ya kwanta a asibiti tsawon wata shida, har ya kai ga an saka masa ƙarfe a ƙafa. Na rubuta littafin, na kai buga wa, ni ma na samu haɗari a daidai inda na rubuta, sannan na kwanta a asibiti tsawon watanni shida, har takai an saka mini ƙarfe (dariya). Saboda fargaba da tsoro har yau ban buga na biyun littafin ba, duk da na gama rubuta shi. Wannan shine abinda bazan taɓa manta wa da shi ba a harkar rubutu.

A yanzu rubutun batsa ya samu wurin zama a duniyar rubutun malam Bahaushe, saɓanin can inda aka fito. Shin akan wa za iya ɗora laifin?
Masu rubutun batsa ba asalin marubuta ba ne, don haka zan ɗora alhakin hakan akan iyayensu. Tunda duk mai tarbiyya ba zai rubuta batsa ba, shi rubutu ana yin shi ne don faɗakarwa, ba wai don shirme ba.

Ko akwai wani shiri da manyan marubuta ke yi don nusar da masu irin wannan rubutun?
Akwai shirin da ake yi a tun kafin yau, shine, an kafa ƙungiyoyi da ‘groups’ a ‘Facebook’ da ‘WhatsApp’, waɗanda duk wani sabon marubuci za a horar da shi yadda zai rubuta labari da ƙa’idojin da zai bi . Kuma ko ya rubuta, kafin ya fitar sai ya tura a ‘group’ an gani, manyan sun tantance kafin a fitar da shi. Wannan shine matakin nusarwa da aka ɗauko, wanda hakan ya daɗe.

Wacce shawara za ki ba wa marubuta masu tasowa?
Shawara ta ga marubuta masu tasowa, su yi koyi da tsofaffin marubuta, su dinga neman shawarwarin waɗanda suka daɗe a harkar rubutu. Sannan kafin su fitar da littafi, su tabbatar an duba mu su inda gyara a gyara, musamman ƙa’idojin rubutun da kuma kiyaye rubutun batsa kamar yadda wasu ɓata gari suke yin basaja a zaci asalin marubuta ne ke rubuta batsa. Su nemi shawara tare da shiga ƙungiyoyi na tsofaffin marubuta da haɗa kai da su kafin wani mataki na fara rubuta littafi.

Mene ne saqonki ga ‘yan’uwa marubuta da ke buga litattafansu, ganin cewa kasuwar ta kwanta?
’Yan uwa marubuta su yi haƙuri. Kar su karaya, su ci gaba da buga littafansu, su kai kasuwa, a hankali komi zai daidaita. Tabbas wata rana kasuwar za ta farfaɗo, idan abin ya juyo. Har yau akwai waɗanda ba sa iya karatun littafi a waya. Su jajirce ko da kaɗan-kaɗan ne a buga, a kai kasuwar, a yi haƙuri, watarana kasuwar za ta farfaɗo. Na tabbatar nan ba da jimawa ba kasuwar littafi za ta dawo kamar da.

Madalla, mun gode.
Ni ma na gode sosai.