Na rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓe, ba zan je kotu ba, inji Kabiru Gaya

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sanatan Kano ta Kudu, Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana cewa ya rungumi ƙaddarar faɗuwa zaɓen Majalisar Dattawa na shiyyar Kano ta Kudu da aka gudanar, wanda Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila na Jam’iyyar NNPP ya yi nasara.

Sanata Kabiru Gaya ya bayyana hakan ne cikin wani saƙon murya da aka raba wa manema labarai a Kano ranar Litinin.

Kabiru Gaya ya kuma taya Kawu Sumaila murnar lashe zaɓen, tare da ba shi tabbacin ba zai ƙalubalanci sakamakon zaven a kotu ba.

”Sau huɗu na ci zaɓen Sanatan Kano ta Kudu, shekaru 16 kenan. Kuma a cikin huɗun nan sau ɗaya kawai aka taba kai ni ƙara kotu sauran ukun ba a kai ni ba. Don haka Ina sanar da Kawu Sumaila cewa ba zan kai shi ƙara kotu ba kuma Ina taya shi murna,” inji Sanata Kabiru Gaya.

Sanata wanda ya yi Sanatan Kano ta Kudu sau huɗu a jere, ya gode wa ɗaukacin al’ummar yankin waɗanda suka haɗar da ‘yan kasuwa, dattawa mata da matasa bisa haɗin kan da su ka ba shi tsawon shekaru 16.