Na san yadda za a daina yunwa Afrika – Buhari

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi iƙirarin cewa, ya san hanyoyin da za a bi wajen daina ƙarancin abinci a Nahiyar Afrika, har ma a riƙa fita da shi zuwa lasashen duniya, ya na mai kira ga shugabannin ƙasasshen Afrika da su himmatu wajen bunƙasa harkokin noma da kiwo a nahiyar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a Jawabin Fatan Alheri da ya gabatar a Taron Ƙara Wa Juna Sani na Shugabannin Gwamnatocin Afrika da aka gudanar shekaranjiya Laraba a Dakar, Babban Birnin Ƙasar Senegal, yana mai yabawa da ƙwazon bankunan Bankin Cigaba na Musulunci da Bankin Raya Afrika (AfDB) da Gidauniyar Raya Noma ta Duniya (International Fund for Agricultural Development) bisa zuba Dala Miliyan 538.5 a harkokin noma a Nijeriya, don aiwatar da Shirin Fita Da Amfanin Gona Zuwa Ƙasashen Waje (SAPZ).

“Ciyar da Nahiyar Afrika shine mafi muhimmanci. Dole ne mu tabbatar da cewa mu na iya ciyar da kanmu a yau, gobe da kuma nan gaba. Turbar da za mu fara hawa ita ce ta haɓaka noma. Hakan na buƙatar samar wa manoma ingantattun kayan aiki, musamman taki mai nagarta da kayan aiki. Kuma tilas mu ba wa manoma tallafi, idan mu na so mu yi nasara. Babu shakka mu na buƙatar ba wa manoma tallafi, amma ta hanyar fayyacecciya, mu cire mugayen halaye irin na masu bayar da bashi kuma mu taimaka wa manoman a aikace.

“Ya kamara a qara yawan kason noma a kasafin kuɗi a dukkan Afrika, musamman ma wajen zuba jari a fannin mafi mahimmancin abincin da aka fi ci da kuma kayan amfani tare da bai wa fannoni mafi muhimmanci a harkar noma, kamar bincike da manyan ayyuka, musamman hanyoyin jigila, noman rani da samar da lantarki.

“A matsayinmu na shugabanni dole ne mu tabbatar da cewa, mun cika alqawarin ware kashi 10% na kasafin kuɗin shekara a ƙasashenmu ga fannin noma, kamar yadda aka cimma a ƙarƙashin Yarjejeniyar Malabo ta Bunƙasa Afrika Tsakanin Shugabannin Ƙasashen Nahiyar.

Tilas mu rage yawan hijirar da ake yi daga karkara zuwa birane ta hanyar bunƙasa harkokin sana’o’in noma,” inji Shugaba Buhari.

Ya kuma ƙara da cewa, “idan mu na son ciyar da Afrika da kanmu, tilas mu na buƙatar matasan manoma mata da maza. Dole mu tabbatar da cewa, sun samu filayen noma, kuɗi, kimiyya da fasaha, cikakkun bayanai da kuma kasuwanni,” yana mai cewa, “babu ɗaga ƙafa kan ciyar da Afrika.”