Na sha wahala a fim ɗin ‘Farida Nabil’ – Haruna Talle Maifata

Daga IBRAHIM HAMISU

Haruna Talle Maifata wani fitaccen jarumin ne da ya yi fice a masana’atar fim ta Kannywood, inda ya fi fitowa a matsayin ɗan daba ko mugu, a tattaunawarsa da Ibrahim Hamisu a Jos, za ku ji dalilan da ya sa ya ke fitowa a mugu da kuma irin nasarorin da ya samu a masana’atar. ku biyo mu:

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?

HARUNA: Da farko dai ni sunana Haruna Talle maifata.

Za mu so jin taƙaitaccen tarihinka?

An haifeni a Jos ta Jihar Plateau, na yi karatun primary da secondary, sannan na yi diploma a ɓangaren Mass Commication, inda na kammala a 2010, to anan na tsaya, amma kuma ina da burin ci gaba.

Ta yaya aka samu kai a masana’atar fim ta Kannywood?


Harkar fim tana bani sha’awa sai naga yayana yana yi mai suna Baban Umma Talle maifata, da mukai magana da shi, sai ya yi min alƙawarin zai sakani fim, Allah bai yi ba, to sai na nemo kuɗina, sai na yi wa Bello Mohammad Bello magama a matsayinsa na director ya jagorance ni na yi nawa fim din. To a haka har fim ya zama sana’a ta.

A wacce shekara ka shiga masana’atar Kannywood?

Na shiga masana’atar a shekarar 2003.

Ko za ka iya tuna fim din ka na farko?

fim ɗina na a farko shi ne ‘Zuciyata’.

Ko za ka iya tuna adadin finafinan da ka yi?

Gaskiya suna da yawan da bazan iya lissafawa ba.

Waɗanda ka yi producing fa?

Waɗanda na yi producing za su kai finafinai Hamsin da uku (53).

Ko za ka iya lissafa mana sunayen wasu daga ciki?

Wasu daga ciki sun hada da: ‘Zuciyata’, ‘Hafsa ko safiya’, ‘Farmaki’, ‘Giwar Ƙarfe’, ‘Dan talaka’, ‘Gidan Maza’, ‘Gidan Alkali’, ‘Farida Nabil’.

Me ya sa a wasu lokutan ka ke fitowa a matsayin ɗan ta’adda?

Yanayin labarin ne yake zuwa a haka, ni kuma sai na yi ƙoƙarin maida kaina haka don labarin ya yi ma’ana.

Wane fim ne ya baka wahala da ba za ka taɓa mantawa da shi ba?

fim ɗin da ya bani wahala shi ne ‘Farida Nabil’.

Wane fim ka fi so a cikin finafinanka?

Gaskiya na fi son fim din ‘Tawalkaltu’.

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu a Kannywood?

Gaskiya na samu nasarori da yawa, domin na yi aure kuma na samu gidaje na yi motoci, na yi yara har hudu. Na kai mahaifiyata ƙasa mai tsarki bayan wanda babana ya kaita da sauransu.

Ƙalubale fa akwai ko babu?

Duk nasara tana tare da ƙalubale don haka nasarorin da na samu a harkar fim ta goge ƙalubalen da na samu don gaskiya babu abinda zan ce sai, Alhamdulillah.

Da wa ka ke koyi a masana’atar Kannywood?

Bana koyi da kowa, domin har yanzu ban ga irina ba, dalilina kuwa shi ne, babu roll din da ban yi ba, tun daga soyayya, abin dariya, mugunta, malanta, da sauransu.

Talle Maifata

Ya batun aure fa matanka nawa?

(Dariya) Matata ɗaya da yara huɗu.

Wane abu ne ka tsana a rayuwarka?

Babban abinda na tsana shi ne ƙarya da kuma cin amana.

Wane abu ne ke sanya ka farinciki?

Wallahi abinda ke sanya ni farinciki shi ne na ga Ina kyauta.

Menene burinka a Kannywood?

Burina shi ne na ga mu na yin finafinai masu inganci waɗanda suke koyar da addinina, wato addinin Musulunci.

Mun gode.

Ni ma na gode.