Na yi ƙoƙarin sasanta Kwankwaso da Buhari don kar ya bar APC – Bala Gwagwarwa

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Hon. Bala Muhammad Gwagwarwa jagoran Jam’iyyar SDP a Kano, ya bayyana cewa a matsayinsa na tsohon ma’ajin Jamiyar APC na Ƙasa daga 2015 zuwa 2019 ya ce rashin fahimtar da aka samu a tsakanin Shugaban Ƙasa Muhammad Buhari da tsohon Sanata kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ta haddasa yunƙurin ficewar Kwankwaso daga APC wanda kuma a ƙarshe ya fice ya koma PDP ya yi iya ƙoƙarinsa na sasanta Shugaba Buhari ƙasa da ƙusoshin APC na ƙasa wanda ya so kada ya fice daga jam’iyyar amma duk da haka Kwankwaso ya qi yadda duk da a cewarsa ya samu nasarar da cikar burin sasanta su.

Hon. Gwagwarwa ya bayyana haka ne a lokacin da yake zanatawa da manema labarai kan dalilan da suka fusata shi ficewa daga jam’iyyar APC ya koma SDP, ya ce da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da ya yarda da shawarar shi haqura da yanzu shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a APC ko kuma mataimakin ɗan takarar shugaban Nijeriya, ko da yake bayan nasarar da ya samu a cewarsa na wannan aiki amma a matakin jiha ne ya samu matsala ta yadda ya fuskanci akwai wata matsala da ban iya shawo kanta ba tsakanin Dakta Abdullahi Umar Ganduje da kuma Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

A ƙarshe ya ce, siyasar ‘yanci suka koya, suka iya kuma ita, sannan suke yin ta, don haka yanzu da ya koma SDP duk ‘yan santsi da sauran jam’iyyu na ta tururuwa zuwa jam’iyyar su wanda yake nuna alamu za su kafa gwamnati a Kano a 2023 inda za su bunƙasa ilimi, noma, kasuwanci, lafiya da sauransu.