Na yi da-na-sanin rera waƙar Abubakar Ladan, Cewar Aminu ALA

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano

Ɗaukar waƙar wani mawaƙi rubutacciya a rera ta ba wani sabon abu ba ne a fagen waƙa a duniya. Don haka ne ma ake samun wasu mawaƙan ko dai su saya ko su nemi izinin rera wata rubutacciyar waƙa da wani mawaƙi ya zauna ya tsara. Irin wannan salo ne fitaccen Mawaƙi Alhaji (Dakta) Aminu Ladan Abubakar (ALA) ya yi amfani da waƙar ‘Afrika’ ta Marigayi Malam Abubakar Ladan Zariya, inda ya rera ta a salo na zamani tare da kayan kiɗa na zamani da nufin zamanantar da waƙar. To, sai dai bayan fitar waƙar wasu abubuwa sun biyo baya, wanda hakan ya sa mu ka ji ta bakin Aminu Ala ɗin, domin jin yadda ya tsara waƙar da kuma abubuwan da su ka biyo baya, inda da farko mu ka fara da tambayar sa bambancin waƙar da sauran waƙoƙin da ya saba rerawa. Sai ya fara amsa tambayar da cewa:

To, wannan waƙar ta ‘Afrika’ tana da bambanci kamar yadda shi mai waƙar, Malam Abubakar Ladan Zariya, wanda shine ya ƙirƙiri fasahar waƙar kuma ya yi waƙar a shekarar 1959, sai kuma aka sabunta ta a 1973. To, shi mutumin Zariya ne, ni kuma a yanzu da na ƙara rera ta mutumin Kano ne. Don haka akwai bambancin karin harshe na Zariya da na Kano, don wani lokacin Zariya za ka ga sun mayar da namiji mace, amma Hausar Kano ana ɗora komai a bigirensa. To, wani lokacin a walar na kan yi ƙoƙarin canja wa karin suna, wani kuma na kan bar shi a yadda ya rera. Na biyu kuma shine ya yi waƙarsa, ya yi binciken sa kafin ya rera. Don haka akwai sunaye da ya jero na shugabannin Afrika. Don haka an samu saɓani, saboda na yi amfani da rubutacciyar waƙar ne, ba wadda ya rera ba, domin ita ban same ta cikakkiya ba, sai guntu-guntu, babu wadda aka samu cikakkiya a kaset, sai littafin waƙar wanda aka buga na samo shi a Jami’ar Ɗanfodiyo. Don haka na ke ganin akwai kura-kurai na keken rubutu. Misali; a cikin littafin akwai inda aka rubuta Mandela, to da na saurari waƙar a wajen da ya ke lissafo shugabannin Afirika ne sai na fahimci Mandela ya ke nufi. Don haka sai ya zama abin da na gani a rubuce da shi na yi amfani. Sannan kuma an yi ta ne a tsarin rubutacciyar waƙa, wadda a ke karantawa cikin zubi da tsari, yadda a ke karantawa kuma ya yi ƙoƙari ya samar da kari nasa na kansa, wanda masana waƙoƙi ne za su san shi ‘Bahrul Dawilu’ ne da sauran su. Amma dai ya karanta ta babu amshi babu kixa. To, ni kuma sai na zo na sa mata kiɗa da rauji irin namu na masu waƙoƙin baka, saboda na isar da abin da na ke so a ji cikin sauƙi.

To, ya aka yi ma tunanin rera waƙar ya zo maka?
Da ya ke ba ya raye aka yi ta ka ga babu maganar neman izini a wajensa ta ɓangaren haƙƙin mallaka, sai dai tunanin su waye suke da gadonsa ko masu haƙƙin mallakarta. Amma dai yadda abin ya samo asali shine, Shugaban Majalisar Malamai ta Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ne ya same ni a ofishina ya ce, buƙatarsa ce ta kawo shi, ya ba ni CD na waƙar Abubakar Ladan ya ce, “Ni masoyin Abubakar Ladan ne. Ina zuwa har gida na gaishe shi na yi masa alheri, saboda fasaharsa, domin aikin da ya yi ba ƙarami ba ne, don ya tabbatar da tarihinmu na lasar Hausa, ya samu dama ya taskace tarihin shugabannin Afrika, wanda ba za mu samu damar yi ba a yanzu. Don kada abin ya tafi a iska ya zama matasa ba su sani ba. Don haka na ke son ka karanta, ka rera ta yadda ka ke yi, don mu amfana, kuma shi ma za a tuna da shi kuma kai ma albarkar waƙar za ka samu wata daraja kuma mutane za su fa’idantu.” To, wannan dalilin ya sa na yi ta, kuma har na yi masa magana akan haƙƙin mallaka, idan an tambaye ni, na ce shine, ya ce na yi, kuma sai na ga ma ai idan waƙa ta shekara 50, to ta tashi daga mallakar mai ita ta koma ta al’umma, sai dai idan ya ƙara sabunta rajistar haƙƙin mallakar. Don haka yanzu ta tashi daga mallakarsa.

To, ya aka yi wajen rera ta da rubutawa tun da ba fasaharka ba ce?
Gaskiya na sha wahala wajen karanta ta. Don ka ga shi a ‘CD’ ya kawo mini, kuma CD ɗin ma ba shi da kyau. Don haka sai da na nemi littafin waƙar kuma na biya kuɗi mai yawa aka je aka bugo CD a Legas kuma da aka buga har zuwa yanzu ba mu sayar da CD 500 ba, kuma na buga 50,000 ne. A yanzu ya na nan a ajiye, ba mu san ranar sayar da shi ba.

To, ko an zo maka da maganar ka saci fasahar wani daga baya?
Gaskiya ne, domin an samu wasu daga cikin ‘ya’yansa, wanda ba zan kama suna ba, amma dai mun yi musayar yawu da su kan cewar za a kai ni ƙara; wai saboda na ɗauki fasahar babansu na yi amfani da ita ba tare da izininsu ba, duk da na yi ta ƙoƙarin fahimtar da su, amma hakan ba ta samu ba. Daga ƙarshe na ce ya tafi kotun ma, amma dai bai je ba, sai daga baya ya kai ni ƙara wajen wasu mutane biyu da na ke ganin ƙimarsu, wato Sani Mu’azu Jos, wanda a ke kira Bawa Maikada a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, da kuma Dakta Aliyu Tilde, wanda Kwamishinan Ilimi ne yanzu a Jihar Bauchi, duk sun kirawo ni sun yi mini magana kuma na yi musu bayani. Har ma shi Dakta Aliyu Tilde ya ke faxa musu cewar, mawaƙa a yanzu ba sa samun kuɗi da waƙa bare su ci moriyarta. Na baya su a ke kirawowa a ce su yi faɗakarwa a kan noma ko kiwon lafiya ko wani abu, kuma gwamnati har ta saurare su ta ba su kuɗi ko ma a ɗauki nauyin su a zagaya da su ƙasashen duniya, amma na yanzu sai dai su yi waƙar siyasa. To, hakan dai ya kawo ƙarshen matsalar tsakaninmu da wasu daga cikin ‘ya’yansa, amma ba su san ba ra’ayina ba ne. Irin wannan waƙoƙin akwai su da yawa a waje na, kamar waƙar Dakta Uba Adamu kundi ne guda ya kawo mini na rera waqar, kamar waƙar Mudi Spikin su na da yawa, mu ba mu yi wanda ya kai su ba kuma ba a san su ba, kuma ya kamata mu riƙa fito da su, don al’umma ta amfana, kamar waƙar Mu’azu Haxeja, Aliyu Aƙilu da su Sheikh Nasiru Kabara da sauransu.

Ya za ka kwatanta wannan waƙar da kuma waɗanda kai ka tsara su ka rubuta su kuma ka rera su?
To, farko dai wannan waƙar na sha wahala, saboda ba ni na ƙirƙiri fasahar ba, kuma sai ya zama shi mutumin da ya ƙirƙiri waƙar ya yi amfani da Boko da Arabiyya a cikin waƙar. Saboda haka akwai wasu kalmomi ma ni sai daga bakinsa na ke jin su, kamar kalmar nahiyoyi misali urubba, kamar Afrika sai ya ce Ifirikiyya, kamar mulkin mallaka, sai ya ce isti’imariyya. Duk waɗannan kalmomin wanda na ji daga bakin sa wasu yare ne ya hausantar da su a cikin waƙar sa. Don haka sai daga baya na gane wasu kalmomin Turanci ne, wasu kuma Larabci ne. Wannan ya sa waƙar ta yi mini tsauri sosai. Don haka ta ba ni wahala.

Duk da wahalar da ka sha a wajen rerewa daga bayaninka na baya sai na fahimci ba ka ci moriyar waƙar ba.
To, ai daga cikin abubuwan da na yi a waƙa, ba don girmama shi malamin da ya saka ni na yi waƙar ba, to irin yadda iyalan Abubakar Ladan suka ɗauke ni da irin yadda suke kallo na a kan waƙar cewar na shiga cikin gadonsu, to da zan iya cewa shine, na yi da-na-sanin ban yi ba, domin a waƙa ba na shiga hurumin mutane, kuma duk abin da na yi zan yi ƙoƙarin na yi abin da ya dace da ni, amma wannan waƙar ba martabata ta ɗaga ba, martabar mahaifinsu ta ɗaga, saboda duk inda ya faɗi abu haka na ke faɗarsa kuma Ina gabatar da sunan sa cewar shine mai waƙar, shi ya rubuta ta. Don haka idan akwai wani abu da na yi a ɓangaren fasaha kuma na yi da-na-saninsa, to wannan waƙar ce. Don na kashe kuɗina masu yawa, amma waɗanda ya kamata su ga na yi musu abin alfahari sune suke ƙoƙarin su ga sun tura ni a gidan yari; wai don suna tunanin na yi amfani da fasahar babansu. Don haka na yi da-na-sani da Allah wadai da aikin wannan waƙar da na yi.

To, mene ne saƙonka na ƙarshe?
Saƙo na dai shine, mutane su riƙa sanin abin arziki, idan an yi musu, domin abin arziki ba da tsiya a ke saka shi ba, kuma Ina alfahari da kasance ta mawaƙi mai isar da saƙo da faɗakarwa. Na gode kuma Allah ya saka da alkhairi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *