Na yi kuskuren ɗaukar Atiku a matsayin mataimakina a 1999 – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Nijeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ɗaya daga cikin kurakuran da ya tafka a rayuwarsa shi ne zaɓar mataimaki a 1999.

Obasanjon ya bayyana haka ne a yayin da yake amsa tambayoyi a wani taro na wasu ɗalibai a Abeokuta da ke Jihar Ogun, ranar Asabar 25 ga Yuni, 2022, kamar yadda jaridar Intelregion ta ruwaito.

Obasanjo dai shi ne ya yi nasara a zaɓen Shugaban Nijeriya a shekarun 1999 da 2003, inda Atiku Abubakar ya zama mataimakinsa.

“Ba zan ce bana kuskure ba, na yi su da yawa,” inji Obasanjo.

“Amma wani abu da ya faru da ni shi ne Ubangiji bai taɓa kunyata ni ba. Kuma wannan abu ne mai muhimmanci.

“Misali, ɗaya daga cikin kurakuran da na yi shi ne ɗaukar mataimaki lokacin da zan zama shugaban ƙasa.

“Sakamakon wannan kuskure ne mai kyau, Ubangiji ya kare ni,” inji Obasanjo.

Kazalika, tsohon shugaban ƙasar ya bayyana cewa a yadda siyasar ƙasar take tafiya ya nuna ƙarara dattawa ba za su bai wa matasa dama wajen fitowa takarar a kujerun siyasa ba

Ya bayyana cewa irin kuɗaɗen da ake facaka ko kashewa a cikin siyasar wannan zamani zai yi wa matasan Nijeriya wahala su iya fafatawa wajen neman wata kujerar da suke sha’awa.

Obasanjo ya ya cigaba da yin kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu haɗin kai da ƙaunar juna, kuma ya yi kira da cewa kada su zama masu nuna bambancin addini.