Na zama marubuci tun a ranar da na fara iya karatu da rubutu – Abul-Waraƙat

A yau wannan fili ya yi babban kamu inda ya karɓi baƙuncin fasihi kuma haziƙin marubuci kuma mawaƙi, wato Binyaminu Zakariya, wanda saboda hazaƙar sa da basirar sa ake yi masa laƙabi da Abulwaraƙat, wato baban takarda. Binyamin Zakariyya ya bayyana cewa ya fara rubutu ne tun daga lokacin da ya fara iya rubutu, wato ya na ƙaramin yaro. Haziƙin ya ƙware wajen rubuta waƙa da rubutun hikaya a harshen Larabci da Hausa. Ku biyo mu don jin yadda tattaunawar mu da shi ta kasance.

Daga IBRAHIM HAMISU Kano

Masu karatun mu za su so sanin taƙaitaccen tarihin ka.
Suna na Binyamin Zakariyya wanda wasu su ka fi sani da Abul-waraƙat. Ni haifaffen unguwar Ayagi ne da ke Ƙaramar Hukumar Dala, cikin birnin Kano. An haife ni a ranar Laraba, 16 ga watan Yuli, a shekarar 1986. Na yi karatun addini da na zamani, inda na yi firamare a Ɗanlami Ibrahim Primary School daga shekarar 1994 zuwa 1999. Sannan na yi sakandire a GAC Gwale daga 1999 zuwa 2005. Bayan haka na halarci Kwalejin Tarbiyyar Musulunci ta College of Islamic Education, Kura. Daga bisani na tafi Jami’ar Bayero daga 2012 zuwa 2014. A shekarar 2018 na koma jami’ar don yin digiri na biyu (Masters) a harshen Larabci. Kuma na yi karatun addini daidai gwargwado, ina ma kan yi.

Yaushe ka tsunduma harkar rubutu kuma me ya ja hankalin ka?
Ban san lokacin ba gaskiya. Tun ranar da na fara iya karatu da rubutu na tsinci kai na ina rubutu. Sai dai na zata wasan yara na ke yi, sai daga baya na gano wata baiwa ce Allah ya yi ta a tattare da ni. Har dai na kai lokacin da na gamsu zan iya isar da saƙon zuciya ta ga al’ummar da Allah ya yi ni a cikin ta.

Littattafai nawa ka rubuta daga lokacin da ka fara rubutu zuwa yanzu?
Ni marubuci ne a yare biyu: Hausa da Larabci, kuma a vangare biyu waqa da kuma rubutun zube. A kowane ɓangare na yi gwargwadon iyawa ta. A dunƙule kuwa zan ce sun kusa ɗari.

A ‘yan shekarun nan an fi jin ɗuriyar ka a fagen rubutacciyar waqa. Shin ka daina rubutun zube ne?
Ban daina rubutu ba, bakin rai bakin fama. Na fi fito da rubutun waƙoƙi na ga al’umma sama da rubutun zube.

Ya zuwa yanzu tsakanin rubutacciyar waƙa da rubutun zube wanne ka fi maida hankali a kai?
Duk wanda ya motsa min sai na karkata gare shi, in ina waqa rubutun zube ya ɗarsu a rai na na kan koma, haka in rubutun na ke waƙar ta faɗo.

Tsakanin rubutacciyar waqa da rubutun zube ya za ka kwatanta sauƙi ko wahalar su?
Duk ba sauƙi, amma wanda Allah ya yassare maka sai ka mayar da shi kamar wasa.

Wai mecece rubutacciyar waƙa ne?
Wani tsararren zance ne da ake samar da shi ta hanyar kula da wasu ƙa’idojin hawa da saukar sauti da amsa amo.

Waɗanne dabaru za ka bayar ga mai shirin fara rubutan waƙa?
Ya takura wa kan sa da sauraren waƙoƙin ƙwararrun da su ke burge shi, sannan ya dinga ƙoƙarin kwatantawa. Amma ilimin harshe jigo ne gare shi, ilimin addini kuma ado ne.

A wane lokaci ka fi jin daɗin rubutu?
Duk lokacin da rubutu ya gayyace ni,ba san da na gayyace shi ba, wato duk lokacin da ina zaune ko ina tafe sai wani tunani ya faɗo min na ji ina son yin rubutu a kai. Saɓanin lokacin da zan ce ina son yin rubutu ni da kai na, to a irin haka ba na jin daɗin rubutu. Amma ni ba a yanayin da ba na iya rubutu – safe, rana da dare, cikin farin ciki ko ɓacin rai ko ma wane yanayi; kawai dai in baiwar ta motsa min shi kenan.

Ka taɓa shiga gasar rubutacciyar waƙa?
Na shiga ta ƙungiyar Poets in Nigeria reshen Jihar Kano, na zo na biyu. Na shiga ta Ƙungiyar Marubuta Da Manazarta Waƙoƙi ta Nijeriya ta ‘Ga Ni-Ga-Ka’, na zo na ɗaya.

Rubutacciyar waƙa gado ka yi ko wani ne ya koya maka?
Ba gada na yi ba, ba koya min aka yi ba, Allah ne ya yassare min.

Ka taɓa samun lambar yabo a sanadiyyar waƙa?
Na samu ta kungiyar PIN da Ƙungiyar Marubuta Da Manazarta ta Nijeriya reshen Jihar Kano, da ta ƙungiyar HAF da sauran su.

Ka na da tunanin samar da littafin rubutacciyar waƙa don yin nazari a manyan makarantu?
Kundi na na farko ‘Alu-Ja’ ya na hanya. Akwai ‘Taɓa-Ka-Lashe’, sannan ina kan tattara na uku.

Waɗanne nasarori ka samu a harkar waƙa?
Nasarar farko ita ce ta samun damar bayyanar da abin da ke rai na ta sigar waƙa, kuma na ke isar da saƙon da ya kan ilmantar ko ya faɗakar ko ya nishaɗantar da jama’a. Bugu da ƙari, shaidojin karramawa da na ke samu su na cikin nasarorin da ba zan manta ba. Haka nasarar da na samu sa’i da lokaci a gasar waƙoƙin da na shiga. Ba abin da zan ce sai alhamdu lillahi.

Ƙalubale fa, akwai ko babu?
Cunkushewar abubuwan da na ke yi don rubutawa, da ƙarancin lokaci da gajiyarwar mutumtaka, sai kuma cunkoson abubuwan da na rubuta na ke burin isar da su ga hannun jama’a, don cikar amfanin su a matsayin gudunmawa ta ga al’ummar da Allah ya yi ni a cikin ta.

Wanene allon kwaikwayon ka a marubutan waƙoƙi ko littafi?
Ina son waƙoƙin Aliyu Namangi, wato ‘Imfiraji’, da na Sa’adu Zungur, Aliyu Aƙilu, Sani Yusuf Ayagi da Mudi Spikin.

Wane kira za ka yi wa marubuta littafi wajen yawaitar rubutu a kan tarbiyya?
Duk marubuci ko mawaƙin da ya san kan sa ya san al’ummar sa, ko ba a ce ya yi waƙa kan tarbiyya ba ya san wannan wajibin sa ne, saboda rubutu da waƙa adabi, shi kuma adabi madubin rayuwar al’umma ne, dole ne kuwa a haska mata kyawawan ɗabi’un da za su kai jama’a tudun mun tsira.

Wane jan hankali za ka yi ga hukumomi da masu ruwa da tsaki a kan rubutu?
Harkar rubutu, musamman rubutacciyar waƙa, durƙushewa ta ke. Duk mai iko ya kamata ya bada gudunmawar farfaɗo da wannan ɓangaren na adabi, kar ya bi sahun ajami. In marubutan tallafi za a ba su ko a dinga sa gasa da za ta motsa su, kamar yadda Jami’ar Ɗanfodiyo a tsukin nan ta sa. Ya kamata ƙungiyoyi da jami’o’i su motso.

Me za ka ce ga jaridar Manhaja?
Ta zo a lokacin da ake buqatar ta. Allah ya taimaka musu a duk lamuran su, ya ba su damar ciyar da adabi da yaren Hausa gaba.

Madalla mun gode.
Na gode, na gode.