NACOTAN ta yi kira da a gina masaƙu a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ƙungiyar Auduga ta ƙasa (NACOTAN) ta yi kira da a kafa majalisar auduga, masaƙu da tufafi (CTG) domin daidaita tsarin da ya dace.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Abuja bayan wani taron ƙarawa juna sani na kwana ɗaya da ya ƙunshi manyan masu ruwa da tsaki inda aka tattauna kan manufofin CTG da aka gudanar a ranar 5 ga Afrilu.

Sanarwar ta fito ne ta hannun Shugaban NACOTAN, Hamma Kwajaffa, shugaban ƙungiyar masu masana’anta ta Nijeriya, Samuel Oloruntoba da babban sakataren ƙungiyar auduga.

Sauran waɗanda suka rattaba hannun sun haɗa da, Folake Oyemade, shugabar ƙungiyar masu sana’ar kaya ta Nijeriya da kuma Adenike Ogunlesi, shugabar ƙungiyar ƙananan masu sana’ar kaya ta Nijeriya.

ƙungiyar ta kuma ba da shawarar cewa baya ga jami’an gwamnati biyu da za su zauna a hukumar ta CTG, sauran mambobi su fito daga kamfanoni masu zaman kansu.

Har ila yau, sun ce taron CTG ya kamata ya kasance da tsarin kasuwanci mai muhimmanci wanda zai dogara da kamfanoni masu zaman kansu.

Daga cikin wasu ƙudurorin har da cewa masu ruwa da tsaki su gabatar da wa’adin da suka dace don aiwatar da kudurorin da aka cimma a taron.

Daga cikin wasu ƙudurorin har da cewa masu ruwa da tsaki su gabatar da wa’adin da suka dace don aiwatar da kudurorin da aka cimma a taron.

Don haka, ƙungiyar ta kuma buƙaci a samar da kwamiti na CTG da yankunan sarrafa su a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “wannan zai taimaka wajen rage tsadar abubuwan more rayuwa a waɗannan yankuna da kuma rage farashi kaya.”

Sun ce dole ne a sami jagoranci mai bin diddigin aiwatar da Dokar Hukuma ta 003, da sauransu.

ƙungiyar ta ce, gwamnati ta keɓe wani asusu na ɓangarori daban-daban na tsarin darajar da ke buƙatar jama’a su yi amfani da wannan damar ta hanyar yin ciniki tare.

“An gano mambobin CTG goma sha ɗaya na da ƙwarewar da ake buƙata, iyawa da aminci tare da manufar cigaba da manufofin cigaban CTG,” inji su.

Sanarwar ta yi nuni da cewa, an gudanar da taron ne tare da haɗin gwiwar hukumar haɗin gwiwa ta Jamus, Deutsche Zusammennarbett, ƙungiyar Tarayyar Turai da ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta tarayyar Nijeriya.

ƙungiyar NACOTAN ce ta shirya taron, tare da CTG a matsayin ɗaya daga cikin masu gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki, da dai sauransu, an ƙaddamar da manufar CTG a shekarar 2014 da 2015.