NAF ta tabbatar da faɗiwar jirgin samanta a Zamfara, an ceto matuƙin jirgin

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau

Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta tabbatar da faɗuwar jirgin samanta (Alpha Jet) a Zamfara wanda aka ce yana kan hanyarsa ta dawowa daga aikin shawo kan matsalar tsaro a tsakanin iyakokin Zamfara da jihar Kaduna ƙaddara ta faɗa masa.

Daraktan Hulda da Jama’a da Yada Labarai na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ran Litinin a Gusau kuma wadda Manhaja ta mallaki kwafinta.

Jami’in ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Yuli, yana mai jaddada cewa fitaccen matuƙin jirgin, Laftanar Abayomi Dairo, ya yi nasarar fita daga jirgin.

A cewarsa, “Ta hanyar amfani da tunaninsa, matuƙin jirgin, wanda ya gamu da mummunar aman wuta daga ‘yan bindiga ya iya guje musu ya nemi mafaka a garuruwan da ke kusa.”

Ya ce ta hanyar amfani da madubin haskaka duhu da wayarsa, Laftanar Jirgin Dairo ya samu nasarar kauce wa wurare da dama na ‘yan ta’addan sannan ya bi hanyar zuwa sansanin rundunar Sojin Nijeriya, inda a ƙarshe aka kubutar da shi.

“Yana da kyau a lura da cewa lokacin da aka samu labarin hatsarin, Babban Hafsan Sojojin Sama, Air Marshal Oladayo Amao, ya ba da umarnin dole a yi dukkan mai yiwuwa don ceto matuƙin jirgin”, in ji Edward.

Ya yi nuni da cewa bisa ga amfani da hanyar ƙwarewa ta rundunar NAF (Intelligence Surveillance Reconnaissance) (ISR) a Turance, da jirage masu saukar ungulu sun bayar da tallafi ta sama ga Sojojin Musamman na NAF da Sojojin Nijeriya waɗanda suka sami damar gano wurin da jirgin ya rikito da kumbon ɗin matuƙin jirgin, da wuraren da ke kusa da kowace alamar matuƙin jirgin.

“Abin farin ciki ne a lura cewa yayin da yake ɓuya, Laftanar Jirgin Dairo ya tabbatar da cewa kasancewar jirgin NAF a kusa da inda jirgin ya faɗi ya taimaka wajen tsoratar da ‘yan ta’addan da ke bayan sa, wanda hakan ya ba shi damar samun mafaka tare da tserewa zuwa wani wuri mai aminci “.

Ya kara da cewa a kwanan nan, Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, GCFR, ya umarci Sojojin Nijeriya da su yi duk abin da ya kamata don fatattakar masu aikata miyagun laifuka a Katsina da Zamfara da Kaduna.

Yana mai cewa, “Domin cika wannan umarnin ne NAF tare da haɗin gwiwar sojojin sama, a cikin makonni 2 da suka gabata sun matse ƙaimi wajen fatattakar ‘yan bindiga da maɓuyarsu, musamman a waɗannan jihohi guda uku.”

Ya ce bayan kai hare-hare ta sama, an fatattaki ɗaruruwan ‘yan fashi tare da lalata maɓuyarsu da dama.

Edward ya ce duk da akasin faɗiwar jirgin da aka samu, NAF ta ci gaba da jajircewa wajen ganin ta cika umarnin da Shugaban Ƙasa ya bayar.