NAFDAC ta garƙame masana’antu 13 a Kano

Daga AISHA ASAS

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta ce ta garƙame wasu masana’antun sarrafa madara a jihar Kano saboda rashin yin rijista da hukumar.

Kodinetan NAFDAC a Kano, Alhaji Shaba Mohammad ne ya shaida wa manema labarai haka jim kaɗan bayan kammala aikin rufe masana’antun a ranar Alhamis.

Jami’in ya ce hukumar ta dukufa aiki wajen ganin ta bankaɗo masu yin jabun kayayyaki suna saida wa jama’a domin kare lafiyar al’umma.

Ya ci gaba da cewa, bayan sun bincika sun gano waɗannan wurare na sarrafa abubuwa mara inganci sai suka sunkuya aiki inda suka rurrufe masana’antun da lamarin ya shafa.

Ya ce yayin aikin nasu, sun rufe masana’antu guda 13 da ake zargin suna yin jabun kayayyaki suna sayar wa jama’a.

Yana mak cewa, za su gudanar da bincike mai zurfe kan batun rufe masana’antun ta yadda a ƙarshen lamari za a ɗauki matakin da ya dace.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *