NAFDAC ta yi gargaɗi akan yaɗuwar maganin cutar kansa na jabu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Qasa (NAFDAC) ta fitar da sanarwar gaggawa ga ma’aikatan kiwon lafiya da sauran jama’a game da wani maganin da ake zargin na jabu ne na maganin daji mai suna “Phesgo 600mg/600mg/10ml”, mai ɗauke da lamba C5290S20.

Wannan gargaɗin ya biyo bayan rahoton wani likita a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Legas (LUTH) wanda ya nuna damuwa game da maganin bayan wani majiyyaci ya kawo masa.

Bayan bincike, an gano cewa wannan magani ya yi kama da wani na jabun da aka saka wa alama a baya, C3809C51.

A cewar NAFDAC, kamfanin ƙera magungunan, Roche, ya duba hotunan samfurin da ake zargin ya kuma tabbatar da cewa na jabu ne.

An gano rashin daidaituwa da yawa, gami da lambar batch ɗin da ke jiki.

NAFDAC ta jaddada cewa jabun magungunan na da matuƙar haɗari ga lafiyar al’umma saboda ba su da inganci kuma za su iya cutar da lafiyar al’umma.