Hukumar Hajji ta Nijeriya (NAHCON) ta ƙayyade N2,999,000 a matsayin kuɗin kujerar Hajji na 2023.
Shugaban NAHCON na ƙasa, Barista Zikirullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan ranar Juma’a a Abuja.
Wannan na zuwa ne bayan da shugabancin NAHCON ya yi ganawa da shugabannin hukumar Hajji na jihohi a hedikwatar hukumar da ke Abuja.