Naira biliyan 370 aka karɓa a matsayin harajin bankuna a cikin shekaru shida ba tiriliyan 89 ba – Emefiele

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya ce jimillar kuɗaɗen shigar da aka tara a matsayin harajin tambari tsakanin shekarar 2016 zuwa 2022 ya kai Naira biliyan 370.7.

A watan da ya gabata, rahoton Gudaji Kazaure ɗan majalisar wakilai kan rashin gudanar da ayyukan gwamnati ko almubazzaranci da kuɗaɗen harajin tambari, ya tayar da tarzoma kan ƙoƙarin da jami’an gwamnati ke yi na “rufewa” kuɗaɗen harajin da aka samu Naira tiriliyan 89.

Kazaure ya yi zargin cewa, CBN, Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) da kuma sashin kula da qa’ida na fadar gwamnatin ne suka haɗa baki wajen hana shi yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari bayanin sakamakon binciken da ya gudanar a kan kuɗaɗen.

Fadar shugaban ƙasar, ta yi watsi da zarge-zargen tare da bayyanasu a matsayin “ƙarya”.

Da yake magana kan batun yayin taron kwamitin tsare-tsare na kuɗi (MPC) a ranar Talata, Emefiele ya ce CBN ba ta hana ko wace Naira tiriliyan 89 ba.

Ya ce bayanin ya zama dole domin ‘yan Nijeriya na buƙatar sanin haƙiƙanin matsayin al’amura ba ƙarya ba.

A cewar Emefiele, “jimillar kadarorin bankunan sun kai Naira tiriliyan 71; jimillar ajiya a bankuna Naira tiriliyan 44”.

“Daga shekarar 2016 zuwa yau, karvar harajin tambari ya kai Naira biliyan 370.686,” inji Gwamnan CBN.

“Hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta tarayya ta raba Naira biliyan 226.451 na kuɗaɗen ga kwamitin rabon asusun tarayya, yayin da ma’auni na Naira 144.235 na cikin CBN.

“Mafi girman tarin tambarin shine Naira biliyan 71, bankin First Bank ya karɓa.”

Emefiele ya qara da cewa CBN ta naɗa wasu manyan kamfanoni guda huɗu na duniya da za su shiga cikin daftarin bankuna domin tantance ko akwai wani harajin da ba a biya ba.

“Idan akwai harajin hatimi da ba a karva ba, bankuna za su biya kobo na ƙarshe,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *