Naira ta faɗo warwas zuwa 730 a Dala ɗaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Nairar Nijeriyar dai ta faɗo zuwa wani sabon matsayi, inda a safiyar Alhamis ɗin nan an sayar da Naira 730 a kasuwar ƙasa, wanda ya ragu da kashi 0.69 idan aka kwatanta da ranar da ta gabata.

Faɗuwar darajar canjin ta biyo bayan matakin da babban bankin ƙasar ya ɗauka na ɗaga darajar kuɗin ruwa zuwa sama da shekaru 20 sama da kashi 15.5 cikin ɗari, wanda ke nuna ƙaruwar kaso 150 daga kashi 14% da aka bayyana a taron MPC da ya gabata.

Farashin da ya kai Naira 730 a dala shi ne mafi girma da aka samu, yayin da ’yan kasuwar suka shaida wa Nairametrics Research cewa suna sayar da Dala ɗaya kan Naira 735 kuma suna saye tsakanin N725/$1 zuwa N730/$1.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *