Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse
Najeriya na fuskantar ƙarancin ruwan sha, wanda hakan ya biyo bayan bincike da masana a harkar ruwa suka gabatar.
Kamar yadda binciken ya nuna matuqar gwamnatocin ba su ɗauki mataki kan matsalar ba jama’a za su fuskantar ƙalubale mai tarin yawa ta fuskar samun ruwan sha.
Waɗannan bayanai sun fito ne a wani taron kwanaki uku da hukumar samar da ruwan sha ta ƙasa ta shirya a jahar Jigawa da nufin samar da bakin zaren.
Wani masani akan harkar ruwan sha, Ambasada Rabiu Dagari wadda shine Babban Darakta a Hukumar hulɗa da ƙasashen waje, a nasa jawabin ya ce Nijeriya tana buƙatar ta samar da hanyoyin samar da ruwan sha mai inganci domin amfanin al’ummarta.
Ya ce matuqar gwamnati ba ta farka ba ta ɗauki matakan kariya akan matsalar akwai yiwuwar jama’a su fuskanci matsalar mawuyacin ƙarancin ruwan sha tsaftatacce.
Ya ƙara da cewar yana da kyau a samar da mafita tun kafin abubuwa su kai ga lalacewa, inda ya ci gaba da cewar sanin kowanne a wannan shekarar an samu ƙarancin ruwan sama savanin yadda ake yi a baya.
Ya ci gabada cewa damina tana kaiwa wata uku, amma a wannan shekara an samu ɗaukewar ruwan sama kafin lokacin ɗaukewarsa, wanda hakan ya haifar da barazana ga al’umma kuma hakan yana nuni ne cewar a kowanne lokaci za a iya samun matsalar ƙarancin ruwan sha da kuma ƙarancin ruwan ƙarƙashin ƙasa da jama’a suke fuskanta.
Ya ci gaba da cewar rashin ruwan na nema ya sa gwamnatin Nijeriya ta yanke shawarar kiran taron masana da nufin samar da mafita, wadda za ta magance matsalar da take tinkarowa.