Namiji tamkar bishiya ne, idan ya faɗi mata da yawa za su shiga matsala- Hauwa Bala Geidam

Ƙarancin imani ne ke sa mata kashe mazajensu, ba rashin so ba – Hauwa Bala Geidam

Yanzu dai mata sun fahimci ma’anar wadda ta zauna za ta ga zannau, domin sun miƙe haiƙan wurin ganin sun taimaki kan su har ma da mata ‘yan’uwan su da su ke cikin mawuyacin hali. A wannan satin shafin mata a yau na wannan jarida mai farin jini ya samu damar zaƙulo wa masu karatu ɗaya daga cikin matasan mata da ke kishin ‘yan’uwan su mata har ma da ƙananan yara. Hajiya Hauwa Bala Geidam mace da ta amsa sunan ta na mace a fagen tausayin marasa ƙarfi. Ku biyo Aisha Asas don jin tattaunawa ta musamman da mu ka yi da uwa ga marayu har ma da ma su uba:

Daga AISHA ASAS

Za mu so ki sanar da masu karatun mu tarihin rayuwar ki.
Sunana Hauwa Bala Geidam, amma an fi sanina da Amnah ko Husaina. Taƙaitaccen tarihin rayuwata shine; an aifeni a Barno, amma na yi rayuwata a Yobe. Na yi firamare da sakandare ɗina a Yobe, na yi difiloma a Yobe, kuma na yi karatuna na matakin digiri a nan jami’ar Yobe, na karanci ‘public admin’. Zan iya cewa rayuwata gabaɗaya a Yobe na yi ta wanda hakan shi ya maida ni cikakiyyar ‘yar Yobe. Na taɓa aure, ina da ‘ya. Ni ‘yar gwagwarmaya ce, mai ƙoƙarin ganin an kare haƙƙin mata da kuma yara kanana. Wannan shi ne tarihina a taƙaice.

Me ki ka sa gaba a yanzu na daga neman na kai?
To game da abin da na sa a gaba wajen neman na kai shi ne; ina ƙoƙari, kuma ina roƙon Allah ya albarkaci kasuwancin da na ke yi, kuma ina aiki da ƙungiyoyi da dama haka. Kuma ina roƙon Allah ya taimakeni inga kasuwancina ya shahara ko ince ya bunƙasa. Kuma ya yi albarka sosai.

A ɓangare ɗaya, kin kasance ‘yar gwagwarmaya wadda ke yaƙin neman kare haƙƙin mata da ƙananin yara kamar yadda ki ka ce. Ko ki na da wata gidauniya ko ƙungiya da ki ke gudanar da waɗanan ayyukan?
Eh, ƙwarai da gaske ina da ƙungiya wadda na ke gudanar da wannan ayukkan a ƙarƙashinta mai suna ‘women on stage initiative’. An ba ta wannan sunan ne ta yi ‘reflecting’ a aikin da ake yi a ƙarƙashinta. Wannan ƙungiyar itace na ke aiki a ƙarƙashinta.

Za mu so jin ire-iren ayyukan da ku ka gabatar ko ku ke kan gabatarwa?
Eh to, mun yi ayukka da dama tun daga lokacin zuwa yanzu, misali, akwai yaran da muka sa a makaranta, akwai waɗanda muke ɗinka wa ‘uniform’, akwai waɗanda muke taimaka wa da abin sana’a, akwai waɗanda muke ba su horo. Sannan akwai batu na JBB ana turo mana da wasu kes (case) wanda za mu karɓa, wanda za mu iya muna yi, wanda ba za mu iya ba muna turawa ga wasu manyan ƙungiyoyi da muke tunanin za su iya. Sannan tsakaninmu muna zuwa makarantu muna koyarwa ta sa-kai. Saboda mu taimaka wurin ba wa yara ilimi da sauransu. To gaskiya muna yin abubuwa da dama. Wannan misali ne daga cikin ababen da muke yi.

A matsayin ki ta mace, ko kin fuskanci ƙalubale a yayin wannan aiki da ki ka fara?
Ƙwarai da gaske na fuskanci ƙalubale da dama, sai dai alhamdu lilla duk mun tsallake su cikin ikon Allah da yardarSa. Kin san duk in da aka ce ke mace ce, kin taɓa aure, sai a dinga yi maki kallon wani abu daban, to amma dai in ka yi haƙuri, ka na addu’a, ka bar wa Allah komai, insha Allah komai zai zo daidai. Munyi haƙuri, mun yi addu’a, kuma Allah ya amsa, kuma ya ba mu nasara a kai. Alhamdu lillahi.

Za mu so jin irin nasarorin da ki ka samu.
Alhamdu lillahi. Nasarori an same su sosai. Alhamdu lillahi. Misali; ‘award’, na samu kambun karammawa guda uku. Na samu a ƙarƙashin ƙungiyar ‘intellecture development’, wani NGO ne. sun ba ni award as ‘volunteer sarvice’. Sa’anan ‘National Orientation Agency’ sun ba ni ‘award’ su ma. Sa’anan kuma lokacin da na ke ‘university’ jami’ar ta ba ni na ‘first lady of the year’. Har wa yau akwai kamfanin da su ka ba ni ‘best life stylist’ na shekara ta 2019. Don haka na samu nasarori da dama, kuma na haɗu da mutane daban daban ta dalilin aikina. Sai dai mu yi hamdalla, mu gode wa Allah.

Wasu su na ganin ana ba wa ‘ya’ya mata tallafi fiye da yanda su ke buƙata, ko me za ki ce kan hakan?
Eh to, wannan tunani ne na mutane, wanda ya kasance na su ra’ayi, amma a zahirin gaskiya ba na tunanin ana ba su fiye da abin da su ke buƙata, sai dai in ce ana ba su daidai abin da su ke buƙata. Tun da dai kin ga mu mata muke da rauni. Duk lokacin da aka ce abu ya tashi mata ne suke zama ‘victim’. Misali; matsala ta kashe-kashen nan da ake yi da sauran su, idan muka duba mata ne ke shan wahalarsu, domin kaso 99 bisa 100 na mata sukan shiga matsala a lokacin da aka ce an shigo a gari an kashe wasu mutane. Bari in ba ki misali ɗaya, a lokacin da aka kashe namiji ɗaya, to tamkar an sare bishiya ne fa, duk ganye da ‘ya’yan itatuwan da ke kai faɗowa za su yi su shiga wani hali. Kashe namiji ɗaya zai yi sanadiyar shigar mata huɗu ko fiye a matsala. Zai iya yiwa baban wata ne shi, mijin wata, ko kuma yayan wata. Don haka ta ko ina idan an taɓa namiji an taɓa mata da yawa. Gaskiya ba na tunanin ana ba su fiye da yanda su ke buƙata, sai dai in ce wata ƙila ana ba su dai-dai yanda suke buƙata, ko ma ƙasa da yanda su ke buƙata.

Wannan ƙungiya ko ta na ƙwatar wa matan da aka yi wa fyade haƙƙinsu, ko ba ya cikin ayyukan ku?
Ƙwarai da gaske ta na ƙoƙari kan wannan, musamman shi abin da ya shafi fyaɗe da sauransu. Mu na ƙoƙari a kai ƙwarai da gaske.

A ‘yan lokutan nan ana samun yawaitar mata da ke kashe mazajen su. Shin ki na ganin ƙarancin soyayya ce tsakanin ma’aurata ke kawo hakan?
Ba za a ce ƙarancin soyayya ba gaskiya, domin da yawa na yin auren soyayya, amma sai labari ya zo cewa ta kashe mijinta. Sai dai mu ce ƙarancin ilimin Muhamadiyya, ko in ce ƙarancin imani. Sai kuma rashin bin dokokin Allah (S.W.A). Domin duk inda aka ce ga dokokin da Allah ya shar’anta wa bawa, to fa rashin bin su ba ƙaramar illa ba ce ga rayuwarsa. Wanda ba zai gane hakan ba sai wata musibar ta saukar ma sa. Kuma yanzu zamani ya zo da sai dai muce Allah ya kyauta. Don haka gaskiya ba ƙarancin soyayya ba ce.

Hauwa Bala Geidam

A fahimtar ki me ke sa maza ƙarin aure?
(Dariya) To gaskiya zan ce suna kwaikwayo ne, tun da sunna ce babba kuma addini ya amince da ita. To duk ma dalilin da ya sa shi ƙarin auren, wanda zai iya yi wa sha’awa ce, ko kwaikwayo kamar yadda na ce, da ma wasu dalilai, kamar rashin gamsuwa da zamantakewar da yake yi da matarsa, wasu ma akwai abin da su ke so da suka kasa samun sa daga wurin matansu, da sauransu. Amma abin da yake da muhimmanci shi ne adalci. Idan zai yi adalci tun da Musulunci ya halasta masa sai ya yi, matuƙar ba ya yi da niyar cin zarafin matar da ta ke gida ba.

Wasu maza na ƙorafin an mayar da hankali kan mata da ƙananan yara a ɓangaren tallafi ko kulawa da gidauniya ko ƙungiyoyi irin na ku ke ba su. Shin me ya sa ba irin su da ke kare haƙƙin maza?
Eh to, ai shi namiji ta ko ina idan muka duba shi ne mai bada kariya ga mata. Shi ne shingenta. Kuma ita mace ta ko’ina tana neman kariya da tallafawa. Idan tana gidansu ne babanta, idan babanta ya rasu, yayanta ko wani jigo na ahalin na ta, idan ta yi aure mijinta, idan mijin ya mutu ko sun rabu, ɗanta ko danginta. Abin lura shi ne; ita mace a ko wani yanayi, yarinta har zuwa tsufa, tana buƙatar kariya daga namiji. Kuma ta na buƙatarshi ko don tsaron mutuncinta. Misali idan mace a hannun Mamarta take, sai ki ji ana ce ma ta ‘yar mace, amma ai namiji ko a hannun mamarsa yake ba za ka ji ana illatashi da hakan ba. Don haka wannan abu ko a addini ya zo mana, su maza ne a sama, sun fi su ƙarfi ta ɓangarori da dama. Sun fi buƙatar kariya da taimakawa, domin mu mata masu rauni ne. shi yasa ake ƙoƙarin ganin an ba su wannan kariyar da su ke buƙata. Amma duk da haka, akwai ƙungiyoyi da dama da su ke ba su tallafi. Misali, mu a nan ƙungiyarmu, ai akwai maza da dama da mu ka ba wa tallafi da sauran su. Kuma akwai da yawa da ke yin hakan. Sai dai kawai an fi ambatar matan ne fiye da mazan.

Me ya ja ra’ayinki har ki ka yi sha’awar buɗe wannan ƙungiyar?
Gaskiya ba zan iya cewa ga sanda na fara wannan aikin ba, sai dai kawai na taso na ji ina da sha’awar in dinga taimaka wa jama’a. musamman ma mata da ƙananan yara. Tun ina yin shi a lokacin da ba shi da wani tasiri sosai, domin na fara shi ne tun ina aji ɗaya a sakandare, bayan da na kai matakin digiri, a lokacin na fahimci abin da mungiya ta ke nufi, da yanda ake tafiyar da ita da sauransu, sai na ga akwai buƙatar ni ma in kafa tawa ƙungiyar don in samu gudanar da aikin cikin tsari, in kuma ba wa wasu dama su shigo don mu taimaka a tare.

Me za ki ce ga matan da ke zaman kashe wando?
Shawaran da zan basu shi ne; su ajiye girman kai, su tashi su nemi na kansu. Kada su dogara da kowa, su yi sana’a komai ƙanƙantarta. Kada su ce komai sai an masu. An dai ce mai nema na tare da samu. Idan mutum ya tashi ya na nema, kuma ya na addu’a, in Allah ya yarda zai samu na rufa wa kai asiri.

Wane irin kaya ki ka fi sha’awar sanya wa?
Hijabi da jallabiya.

Wace kala ta fi birge ki?
Ina matuƙar son kalar bulu ko wace iri ce, da kuma baƙi.

A ɓangaren abinci, wane ne zaɓin ki?
Abincin gargajiya.

Mene ne babban burinki?
In na tashi mutuwa na cika da imani kuma na gama da kowa da duniya lafiya.

Wace shawara za ki bai wa mata da suka samu kansu a halin cin zarafi na fyaɗe?
Su zama masu haƙuri da rungumar ƙaddara, su dage da addu’a sosai.

Mun gode da lokacin ki.
Nima na gode sosai.