Narendra Modi ya buƙaci haɗin kai don kawo ƙarshen yaƙin Ukraine a taron G20

Firaministan Indiya Narendra Modi ya buƙaci haɗin kan ƙasashe da kawo ƙarshen rarrabuwar kan da yaƙin Ukraine ya haddasa wanda ya ce yana ƙoƙarin jefa duniya a gagarumar matsala, dai dai lokacin da ake buɗe taron ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki da ƙasar ke karbar baƙonci.

A jawabinsa wajen bikin buɗe taron ƙasashe 20 mafiya ƙarfin tattalin arziki da ke gudana birnin New Delhi, Modi ya ce idan aka duba matsalolin da aka fuskanta a fannoni da dama kama daga tattalin arziki qarancin abinci da kuma hada-hadar kuɗi baya ga sauyin yanayi da kuma ƙaruwar ayyukan ta’addanci a shekarun baya-bayan nan, hakan manuniya ce ta bulatar da ake da ita wajen haɗa kai don yaƙar waɗannan ƙalubale.

Narendra Modi ya ce na wannan karo ya zo a dai dai lokacin da ake fama da matsalar rarrabuwar kai tsakanin ƙasashe, kuma dukkanin ƙasashe na da tasu matsayar da kuma yadda suke hangen za a iya warware rikicin, haka zalika manyan ƙasashe ke da alhakin bayar da kariya ga waɗanda yaƙin ya shafa.

Indiya wadda ke jagorancin ƙungiyar ta G20 a bana, na son shugabancinta ya karkata kan batutuwa masu alaƙa da yaqi da talauci da kuma kawo ƙarshen ƙalubalen dumamar yanayi, sai dai da yiwuwar batutuwa masu alaƙa da rarrabuwar kai saboda yaƙin Ukraine su mamaye zaman taron.

Taron na G20 dai sakataren wajen Amurka Antony Blinken da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov waɗanda za su gana da juna karon farko tun bayan haɗuwarsu ta watan Yuli.

Ƙasashen yammaci dai na cike da fargabar yiwuwar Chana ta fara taimakawa Rasha da makamai lura da kasancewarsu ƙawayen juna dalilin da ya sanya gudanar da wani taron manema labarai a wani ɓangare na taron G20 don kira ga Beijing game da wannan yunƙuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *