Nasarawa 2023: Zan bai wa masarautun gargajiya fifiko – Yakubu Maidoya

Daga JOHN D. WADA, A LAFIYA

Ɗan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa a Jam’iyyar NNPP, Alhaji Abdullahi Yakubu Maidoya, ya ce idan al’ummar jihar suka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe zai tabbatar ya inganta tare da ɗaukaka harkokin masarautun gargajiyar jihar baki ɗaya ta yadda za su yi daidai da zamani ba kamar yadda lamarin yake a yanzu ba.

Yakubu Maidoya ya bayyana haka ne a ci gaba da kamfen ɗinsa da yake yi a lokacin da ya ziyarci masarautar Keana, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Keana da ke jihar.

Da yake bayyana wa Sarkin Keana, wato Osana na Keana Mai Martaba Abdullahi Amegwa Agbo maƙasudin ziyarar, Maidoya ya ce da shi da tawagarsa sun yanke shawarar ziyartar sa ne don neman albarkarsa don samun nasara a yaƙin neman zaɓe da yake ci gaba da yi a duka lungu-lungu da saƙo-saƙon jihar baki ɗaya.

Ya ce ba shakka a yanzu masarautun jihar ciki har da na Keana an yi watsi da su inda ake ci gaba da rage darajar su maimakon ɗaukaka su.

Shi ya sa a cewarsa tuni ya sha alwashin yin duka mai yiwuwa idan ya zama gwamnan jihar wajen ɗaukaka martabarsu ta biyan su cikakken haƙƙoƙinsu a matsayin su na iyayen gari.

Ya ce akwai abubuwan more rayuwa da dama da ya kamata gwamnati mai ci yanzu a jihar suna yi wa sarakunan gargajiya amma ba sa yi inda ya ce da zarar ya zama gwamna ba zai yi wata-wata ba wajen aiwatar da waɗannan kyawawan tsare-tsaren gwamnatinsa da suka shafi sarakunan garganiyarn a jihar baki ɗaya.

Ɗan takarar ya kuma sanar wa basaraken cewa gwamnatinsa za ta gina sabbin makarantu da asibitoci da haɓɓaka ɗimbin ma’adinai da albarkatun ƙasa da Allah ya albarkaci garin Keana da kewayenta da su da sauran su kuma duk za a yi ne a kyauta don amfanar al’umma a kowacce masarautar gargajiya a jihar tare da samar musu da ishesshen tsaro musamman tsakanin Fulani makiyaya da manoma da sauran ƙabilu mazauna yankunan.

Daga ƙarshe sai ya jinjina wa Sarkin Keana Alhaji Abdullahi Amegwa Agbo dangane da kyakkyawar jagorancin da yake yi wa al’ummarsa na Keana inda ya buƙace shi ya ci gaba da hakan.

A nasa ɓangaren, basasarken ya gode wa ɗan takarar da tawagarsa dangane da ziyarar na musamman da suka kawo fadarsa, ya kuma bayyana Maidoya a matsayin cikakken ɗan masarautar Keana wanda a cewarsa ziyararsa ta kasance tamkar ya zo gida ne.

Daga bisani ɗan takarar ya kuma ziyarci wasu gundumomin zaɓe da dama da ke wasu yankunan rayawar Keana da suka haɗa da Giza da Agaza da Aloshi da Keana da sauransu.