Nasarorin Sin a gida na da tasirin bunƙasa haɗin gwiwar ta da ƙasashen Afirka

By CMG HAUSA

Mai fashin baki kan harkokin siyasa da tattalin arziki, dan ƙasar Congo (Brazzaville) Alphonse Ndongo, ya ce irin nasarorin da ƙasar Sin ke samu a cikin gida, za su ci gaba da ingiza moriyar da ake samu, daga haɗin gwiwar ta da ƙasashen Afirka.

Ndongo ya bayyana hakan ne a kwanan baya, yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua. Yana mai cewa, albarkacin ƙasar Sin, da yawa daga ƙasashen Afirka sun bunkasa, kuma Sin da ƙasashen nahiyar na ci gaba da morar juna cikin gwamman shekaru.

Masanin ya ce, Afirka ta ci gajiya mai tarin yawa, albarkacin haɗin gwiwar ta da kasar Sin, musamman ma a fannonin raya ababen more rayuwa, da cinikayya da ayyukan gona.

Fassarawa: Saminu