
Daga BELLO A. BABAJI
An samu tsaiko game da ƙorafin kiranyen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya da aka shigar wa Hukumar Zaɓe (INEC), bayan da hukumar ta ce akwai wasu sharuɗɗa da ƙorafin ya gaza cikawa.
Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Labarai da Ilimantar da Masu zaɓe, Sam Olumekun ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Alhamis.
Ya ce, za su yi aiki ne da ƙorafin a ƙarƙashin dokar ƙasa, wadda ta bada damar hakan, saboda haka sai an cika ƙa’idodin da ta gindaya kafin hukumar ta yi aiki a kai.
Olumekun ya ce, sun karɓi kundin takardu shida na ƙorafin daga ƴan mazaɓar Kogi ta Tsakiya ɗauke da sanya hannun sama da rabin masu zaɓe 474,554 daga ƙananan hukumomi biyar da ke ƙarƙashin mazaɓar.
Saidai, a yayin haka, INEC ta lura cewa wakilan da suka kawo ƙorafin ba su bada bayanansu da suka haɗa da adireshi, lambobin waya ko Imel ba, waɗanda ta nan ne za a iya neman su kamar yadda doka ta bayyana, ya na mai cewa na mutum ɗaya aka samu a madadin baki ɗaya wakilan.
Don haka ne hukumar ta ce lallai sai an cika ƙa’idodin kamar yadda dokar ta ayyana don kauce wa abinda ka iya zuwa daga baya a sakamakon saɓa wa wani sharaɗi.
A wani ɓangaren, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta musanta batun da ke yawo na cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya ba ta miliyan N500, lamarin da ta ce ƙarya ne da aka ƙirƙira don a kawar da hankulan al’umma, da kuma ƙoƙarin bata mata suna.
A sanarwar da ta fitar a ranar Talata, Natasha ta ce hakan bai taɓa faruwa tsakanin ta da Akpabio ba, ta na mai kira ga al’umma da su yi watsi da labarin ƙaryar da ake yaɗawa akan ta.
