
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar batun ƙorafin kiranye da ƴan mazaɓarta suka shigar wa hukumar akanta.
A wani saƙo da aka aika wa Natasha, da ke ɗauke da sanya hannun Sakatariyar INEC, Rose Oriaran Anthony, ta ce matakin karɓar ƙorafin da hukumar ta ɗauka, ya ta’allaƙa ne da sakin-layi na 69 na dokar ƙasa a kundin 1999.
Haka ma sanar da ita batun, wanda sashe na 2 na dokokin hukumar na 2024 ne ya bada dama, sannan an wallafa batun a shafin yanar gizo na INEC.
Saidai, ƙorafin bai samu sanya hannu da sauran bayanan wakilan waɗanda suka shigar da shi ba, waɗanda doka ta umarci a yi.
Ta ce, lallai sai an samu sanya hannu daga sama da kaso 50 na ƴan mazaɓar sanatar, kafin ɗaukar mataki na gaba, wanda ta ce za a gudanar a ƴan kwanakin nan tare da sanar da al’umma.
Bugu da ƙari, za a tabbatar da kiyaye gaskiya da adalci a yayin aiki kan ƙorafin, kamar yadda Kwamishinan Labarai da Ilimantar da masu zaɓe, Sam Olumekun ya bayyana a yammacin ranar Laraba.