NATO ta buƙaci gwamnati ta sa baki a batun cin mutunci mambobinta a Keffi

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Ƙungiyar masu motocin sufuri ta ƙasa da aka fi sani da NATO shiyyar ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, ta yi kira na musamman ga hukumomin ƙaramar hukumar ta Keffi da na jihar bakiɗaya su sa baki a batun cin mutunci da cin zarafin mambobinsu da ’yan takwararsu na ƙungiyar NURTW a ƙaramar hukumar suka yi kwanakin baya.

Shugaban ƙungiyar ta NATO a ƙaramar hukumar Keffi, Aalhaji Maiwada Sidi ne ya yi wannan kira a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke sakatariyar ƙungiyar a kan hanyar Keffi zuwa Kaduna a garin Keffi ranar Litinin 17 ga watan Janairun 2022.

A cewarsa, kiran ya zama wajibi idan aka yi la’akari da jinkiri da ake samu wajen aiwatar da hukuncin kotu a kan batun.

Ya ce, bayan wannan cin mutunci da ’ya’yan ƙungiyar NURTW sun yi musu da har ya kai ga farfasa musu motoci tare da raunana wasu daga cikin su ƙungiyar ta shigar da ƙara a wani babban kotu da ke garin ta Keffi inda daga bisani kotun ta yanke hukunci da ya bayyana nasarar ƙungiyarsu ta NATO ya kuma umurci ƙungiyar NURTW ta biya su diyyar kimanin naira miliyan 11 da dubu hamsin.

Amma a cewarsa, har yanzu ba a aiwatar da hukuncin ba. Alhaji Maiwada ya cigaba da bayyana cewa, “shi yasa na ke so in yi amfani da damar nan in yi kira ta musamman ga gwamnatin mu a ƙaramar hukumar nan da na jiha baki ɗaya ƙarƙashin jagorancin mai girma gwamnanmu mai adalci, Injiniya Abdullahi Sule cewa su sa baki cikin batun don abi mana haƙƙinmu kamar yadda kotu ya umurta.”

Dangane da nasarori da ƙungiyar ta NATO a shiyyar ƙaramar hukumar Keffi da kewayenta ta cimma a ƙarƙashin jagorancinsa, Alhaji Maiwada Sidi ya bayyana cewa, wasu daga cikin nasarorin sun haɗa da buɗe shiyoyin ƙungiya wanda shi da kansa ya yi a wasu garuruwa da suka haɗa da Nasarawa, Toto, Loko Maraban Udege da sauransu tare da tabbatar da haɗin kan mambobinsu a ƙaramar hukumar da sauransu duk a cikin waɗannan shekaru da ya yi yana jagorancin ƙungiyar. A ƙarshe ya yi amfani da damar inda ya buƙaci gwamnatoti a duka matakai su riƙa kare rayuwa da dukiyoyin mambobinsu baki ɗaya musamman daga hannun ’ya’yan ƙungiyar NURTW a shiyyar da jihar baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *