Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa, ba a ajiye na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a wuraren da ‘yan bangar siyasa su ka kai hari tare da ƙona su kwanan nan ba.

INEC ta kuma ce wasu muhimman kayyakin da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓukan 2023 su na nan lafiya ƙalau cikin tsaro.

Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wani shiri na gidan Talabijin na Channels a Lahadin da ta gabata.
Okoye ya sake nanata cewa za a gudanar da babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa duk da hare-haren da aka kai wa ofisoshinta.

Hukumar zaɓen ƙasar ta koka kan yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa, inda adadin ofisoshin da abin ya shafa ya kai 50, a faɗin jihohi 21.

Sai dai yayin da yake magana a jiya, Okoye, ya ce muhimman kayan da za a tura domin zaɓen baɗi ba sa cikin wuraren da aka kai harin kwanan nan.

“Ina so in tabbatar wa al’umma cewa kayanmu masu mahimmanci ba sa cikin waɗannan wuraren da waɗannan hare-haren suka faru.

“Mun tabbatar da tsaron tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) da sauran wasu muhimman abubuwa da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen.

”Waɗannan kayan ba sa cikin waɗannan wuraren da ake kai wa hari,” inji Okoye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *