NAWOJ ta taya Raɗɗa murnar cika shekara ɗaya kan karagar mulki

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙungiyar Mata ‘yan Jarida ta Nijeriya (NAWOJ), reshen jihar Katsina, ta miƙa saƙon taya murna ga Gwamna Dikko Umar Raɗɗa bisa cikar sa shekara guda kan karagar mulki.

Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabar ƙungiyar, Hannatu Mohammed da kuma sakatariyar ƙungiyar, Faith Awa Maji.

NAWOJ ta yaba wa Gwamna Raɗɗa bisa irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban jihar, musamman wajen bai wa mata ƙarfin gwiwa wajen ganin sun cimma burinsu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Mai Girma Gwamna, wa’adin mulkinka ya samar da kyakkyawan yanayin kasuwanci, tare da yin amfani da ƙwarewar da kake da ita wajen sanya Jihar Katsina a matsayin cibiyar bunƙasar tattalin arziki a Nijeriya.”

Ƙungiyar ta kuma yi alƙawarin ba da goyon baya ga shirye-shiryen gwamnan tare da fatan ci gaba da haɗin gwiwa.

“Ina taya mai girma Malam Dikko Umaru Raɗɗa murna. Allah ya ja zamanin jihar Katsina da kuma Tarayyar Nijeryia.

Kazalika, ƙungiyar ta bayyana farin cikinta kan nasarorin da gwamnan ya samu da kuma kyakkyawan fata ga makomar jihar.