NBC ta buƙaci gidajen rediyo da talabijin su dai amfani da Tiwita

Daga WAKILINMU

Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), ta bai wa tashoshin rediyo da talabijin na faɗin Nijeriya umarnin dakatar da yin amfani da Tiwita.

NBC ta ce ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan dakatar da Tiwita a Nijeriya da Gwamnantin Taray ta yi kan yadda ta ce kafar ba ta mutunta Nijeriya.

Hukumar ta buƙaci tashoshin da su hanzarta katse shafukansu a manhajar Tiwita a matsayin hanyar tattara bayanai da yaɗa harkokinsu.

Muƙaddashin Babban Daraktan hukumar, Farfesa Armstrong Idachaba, shi ne ya ba da wannan umarni a Abuja a Litinin da ta gabata.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*